Bayan Kwana Uku Da Dawowa Daga Russia, Buhari Zai Tafi Saudiyya

69

A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa Riyad, babban birnin Saudiyya, don halartar wani taron tattalin arziƙi da aka yi wa laƙabi da Future Investment Initiative, FII 2019.

Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce Kamfanin Zuba Jari na Saudiyya, PIF, shi ya shirya taron.

Mista Shehu ya ce taron mai taken: ‘Mene Ne Abu Na Gaba A Kasuwancin Duniya?’ za a yi shi ne tsakanin 29 ga Oktoba zuwa 31 ga Oktoba, kuma zai mayar da hankali a kan manyan abubuwa guda uku: Gaba Mai Ɗorewa, Fasaha Don Ci Gaba Da Al’umma Mai Ci Gaba.

Mista Shehu ya ce taron na kwana uku zai gudana ne ƙarƙashin kulawar Hadimin Masallatai Biyu Masu Alfarma, Sarki Salman bin Abdul’aziz na Saudiyya da kuma Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman bin Abdul’aziz da PIF.

Yariman Mai Jiran Gado kuma shi ne Mataimakin Firimiya, Majalisar Tattalin Arziƙi Da Harkokin Ci Gaba ta Saudiyya.

“Sakamakon samun ƙarin ƙwarin gwiwa da masu zuba jari su ka samu a tattalin arziƙin Najeriya, Shugaba Buhari zai yi amfani da taron don yin jawabi game da damammakin tattalin arziƙi da ake da su a Najeriya, ingancin manufofin gwamnatinsa wajen bunƙasa kasuwanci, ya kuma gayyaci masu zuba jari zuwa Najeriya.

“Ya kamata a lura cewa jimillar jarin da ya shigo Najeriya ya ƙaru daga dala biliyan 12 a wata shidan farko na 2018 zuwa dala biliyan 14 a wata shidan farko na 2019”, in ji hadimin na Shugaban Ƙasa.

A cewar Mista Shehu, tawagar Najeriya za ta duba damammakin da PIF na Saudiyya ke da su, wanda ke ƙoƙarin zama ɗaya daga cikin manya-manyan taskokin dukiyar duniya masu tasiri.

Ya ce tawagar za kuma ta nemi zuba jari daga ƙasashen waje a manya-manyan ayyuka a ɓangaren mai da iskar gas na ƙasar nan, musamman Fayif na Gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano, AKK, gas Pipeline, fayif na iskar gas mai tsawon kilomita 16 da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC yake ginawa a halin yanzu.

“Jami’an Najeriya za kuma su yi amfani damar taron wajen jawo tattaunawa game da shirin Kamfanin Man Fetur na Saudiyya, Aramco, na nuna sha’awa wajen farfaɗo da matatun mai na Najeriya da kuma sabbin zuba jari a fannin man fetur da gas”, in ji shi.

Fiye da wakilai 4000 ne daga ƙasashe sama da 90 ake sa ran za su halarci FII 2019, wanda zai ɗauki nauyin tarukan bita har 12 a kan batutuwa daban-daban da su ka haɗa da birane, makamashi, yanayi, lafiya, bayanai, zirga-zirgar jama’a, abinci, tafiye-tafiye, wasanni, kantina da matasa.

Mista Shehu ya ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar Gwama Babagana Zulum na jihar Borno; Abubakar Bagudu na Kebbi da Aminu Masari na Katsina.

Haka kuma a cikin tawagar Shugaban Ƙasar akwai Ƙaramin Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Zubairu Dada; Ministan Ma’aikatu, Kasuwanci da Zuba Jari, Niyi Adebayo; Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Ibrahim Pantami.

Sauran sun haɗa da mai ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Fannin Tsaro, Babagana Monguno; Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Sirri, Jakada Ahmed Rufa’i Abubakar da Babban Manajan Darakta na Kanfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, Mele Kolo Kyari.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar ya ce bayan kammala taron na masu zuba jari a Riyad, Shugaba Buhari zai wuce Maka, bisa rakiyar wasu hadimansa na kusa don yin Umara kafin ya dawo Abuja.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan