Kwankwaso Gwani Ne A Ta’addanci – Jafar Sani Bello

579

Tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP Jafar Sani Bello ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso gwani a harkar ta’addanci a fagen siyasa.


Jafar Sani Bello ya bayyana hakan ne a shafin sa na fasebuk, a matsayin martani ga harin da aka kaiwa magoyan bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso akan hanyarsu ta dawowa daga gurin bikin kaddamar da makarantar koyon aikin jinya da madugun Kwankwasiyya ya samar a garin Kwankwaso da ke yankin ƙaramar hukumar Madobi.

“ta’adanci a siyasa ba ci gaba bane. Amma fa Kwankwaso gwanin taaddanci ne. A 2014 ya sa an far mana a offishin jamiyya in da Allah ya yi da kwanan mu agaba. Ni an min mumunan rauni a wuya, Rabi Sharada, Dattijo Dauda Dangalan da mutane da dama sun sami munanan raunuka. Allah ya sauwake” in ji Jafar Sani Bello.


Jafar Sani Bello wanda tsohon yaron Rabi’u Kwankwaso ne a siyasance, sai dai kuma an samu tsamin dangantaka tsakanin matashin ɗan siyasar in da kowa ya ke zaman kan sa a siyasance.


Idan za’a iya tunawa dai makwanni biyu da su ka gabata ne aka kaiwa ƴan Kwankwasiyya hari akan hanyarsu ta dawowa daga garin Kwankwaso, wanda jagoransu ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ce ke da alhakin kai musu wannan hari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan