Mara Lafiya Na Buƙatar Miliyan 15 Don Yi Masa Dashen Ƙoda

245

Shekara 18 kenan Mahmud Aminu Daneji, wani mara lafiya mai fama da ciwon ƙoda ya yi yana fama da yadda zai samu lafiya.

Mista Daneji, ɗan shekara 46, wanda ya tattauna da jaridar Kano Focus a kan injin wankin ƙoda a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, AKTH, ya ce a shekara ta 2001 ne ƙodojinsa biyu su ka daina aiki bayan ya samu hawan jini.

“Mutum ne ni mai lafiya da kuzari kafin hawan jini ya kwantar da ni. Ina rayuwata dai-dai kafin jinina ya hau zuwa 220 a watan Maris, 2001”, ya tuna haka.

Ya ƙara da cewa duk da ya daɗe a asibitin yana karɓar magani, tsanantar hawan jinin ce ta lalata ƙodojinsa.

Dashen Ƙoda Da Bai Yi Nasara Ba

Mista Daneji, mazaunin unguwar Daneji a ƙaramar hukumar Kano Municipal ta jihar Kano, ya bada labari cewa daga 2001, an wanke masa ƙoda sau 476 har zuwa Oktoba na 2006 lokacin da aka yi masa dashen ƙoda.

Ya ce bayan dashen ƙodar, wanda ya yi nasara, ya samu lafiya inda ya ci gaba da rayuwarsa ba tare da wani ciwo ba.

“Sai na ji kamar na samu sabuwar rayuwa. Matsalolin lafiyata duk su ka ɓata. Zancen gaskiya ma, na yi aure shekara biyu bayan dashen ƙodar, kuma komai ya yi dai-dai”, in ji shi.

Sai dai kash! A hankali a hankali sai rashin lafiya ya dawo a watan Oktoba na 2010, lokacin da gaɓar da aka dasa ita ma ta lalace. Kuma kamar wani fim mai ban tsoro, sai baƙin cikin Mista Daneji ya zama sabo.

Tun lokacin, wanda yake da ɗa ɗaya, ya ce an yi masa wankin ƙoda sau 987, kuma har yanzu yana ci gaba da ƙirgawa.

Kowane wankin ƙoda, a cewarsa, yana ci masa kuɗi N17,100 har lokacin da AKTH ya lura da matsalarsa, ya yi masa ragin kaso 50 cikin ɗari, abinda ke nufin a yanzu yana biyan N8,550 sau biyu a mako.

Wanda ke zaune da a kan kujerar marasa lafiya, Mista Daneji ya ce ya rasa komai har da gidansa.

“Abinda kawai ya rage min su ne matata da ɗana ɗan shekara 11″, ina rayuwa ne don su” muryarsa tana fita da ban tausayi.

Abinda Yasa Nake Buƙatar Miliyan 15
A ta bakin Mista Daneji, dashen ƙodar da aka yi masa na farko bai yi nasara ba, kamar yadda likitansa ya faɗa masa, yana da wata halitta ta gado wadda ke hana shi karɓar dashen sassa daga wasu.

Rashin lafiyar Mista Daneji ta ƙara rikicewa saboda banda tsarin halittar jikinsa, an yi masa ƙarin jini da yawa, wanda shi ma wani ƙalubale ne.

“Lokacin da na yi gwaje-gwajen HLA Tissue Typing Tests, likitoci su ka ban shawara cewa jikina ba zai karɓi dashen sabuwar ƙoda ba da kaso 68 zuwa 70 cikin ɗari saboda tsarin halittar jikina ta gado da kuma ƙarin jini mai yawa”, a kalamansa.

Taimako A Indiya
Amma, har yanzu akwai fata ga Mista Daneji saboda wani asibiti a Indiya- Apollo International Kidney Centre, wanda yake a New Delhi, ya yi tayin taimaka masa a kan kuɗi Naira Miliyan N15.

“An ba ni shawara da in nemi magani a asibitin Indiya wanda yake da ƙwararrun masana ciwon ƙoda waɗanda za su iya warware matsalata.

“Wannan shi yasa nake neman taimako daga gwamnati, mutane na gari, masu tallafa wa jama’a da ƙungiyoyi da su tara Miliyan N15 don in nemi magani a Indiya”, ya ƙara da haka.

Hajiya Hauwa Abdullahi, mai magana da yawun AKTH, ta ce duk wanda yake son taimakon Mista Daneji, zai iya kai taimakon ta Ofishin Walwalar Jama’a na AKTH.

“Waɗanda su ke son taimaka wa Mahmud Daneji za su iya tuntuɓa ta ko kuma su bada taimakon ta Ofishin Walwalar Jama’a na AKTH”, ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan