Matar Tafawa Balewa Ta Rasu

239

Hajiya Jummai Aishatu Abubakar, matar da ta rage a cikin matan marigayi tsohon Firaministan Najeriya, Abubakar Tafawa Balewa ta rasu.

Ta rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti mai zaman kansa da ke Legas, tana da shekara 85 a duniya, wata majiya ta kusa da marigayiyar ta shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN haka.

Tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa iyalin marigayi tsohon Firaministan, al’ummar Bauchi da dukkan ‘yan Najeriya ta’aziyyar wannan babban rashi.

A wani saƙo da ya aika ta hannun gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, Shugaba Buhari ya ce: “Na ji baƙin cikin jin rasuwar Hajiya Jummai Tafawa Balewa. A wannan rashi nata, Najeriya ta rasa wata gogaggiyar ‘yar siyasa wadda ta damu da matsalolin iyali da kuma wasiyyar marigayi mijinta.

“Ina gabatar da saƙon ta’aziyyata ga iyalan marigayiyar, gwamnati, al’ummar jihar Bauchi da al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Allah Ya ji ƙan ta”.

Shugaba Buhari ya umarci Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapa, da ya bayar da ɗaya daga cikin jiragen Shugaban Ƙasa don ɗakko gawar matar marigayi Firaministan daga Legas zuwa Bauchi, inda za a yi mata jana’iza ranar Litinin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan