Maza Masu Sanƙo Sun Fi Ɗaukar Hankalin Ƴammata – Bincike Masana

2384

Wani binciken masana da aka gudanar ya bayyana cewa maza masu sanƙo sun fi ɗaukar hankalin mata fiye da sauran maza masu gashi. Binciken ya gano cewa masu sanƙon sun fi sauran mutane ilimi da wayon zaman duniya, da kuma iya mu’amala.

Tun da farko dai wani babban Farfesa ne mai suna Frank Muscarella na jami’ar Barry da ke jihar Miami, Florida, a ƙasar Amurka ne ya jagoranci wannan bincike.


Wannan Farfesa ya bayyana cewa a lokacin da sauran mutane ke ganin mutane masu gashi sun fi bawa mutane sha’awa, Farfesan ya ce haka suma maza da suke da sanko sun fi iya mu’amala da jama’a.

Haka kuma binciken ya gano cewa maza masu sanko sun fi bawa mata sha’awa ta in da zaka ga yawancin su suna da girman jiki da kuma karfi fiye da sauran maza.


A ƙarshe sakamakon binciken masanan ya tabbatar da cewa maza masu sanƙo sun fi sauran maza ilimi da kuma gogewa a harkar rayuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan