Wani kamfanin hada-hadar tufafi na Kano, Mudassir & Brothers, ya ce ya fara shirye-shiryen kafa kamfanin saƙa tufafi da zai laƙume Dalar Amurka Miliyan $50 a jihar.
Da yake bayyana shirin kafa kamfanin a wani taron manema labarai ranar Asabar a Kano, Shugaban Kamfanin, Mudassir Abubakar, ya ce sun yanke wannan hukunci ne don tallafa wa manufar Shugaba Muhammadu Buhari ta ƙarfafa gwiwar samar da kayayyaki na gida masu inganci, samar da dukiya da samar da ayyuka ga matasa.
Mista Abubakar, wanda shi ne Babban Jami’in Zartarwa na Kamfanin, ya kuma bayyana cewa tuni Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya amince da bada fili mai faɗin hekta 22.5 don kafa kamfanin.
A cewar sa, idan aka kafa kamfanin, zai iya samar da ayyuka ga matasan Kano fiye da 10,000 da ma na sauran jihohi.
Ya lura da cewa kafa kamfanin saƙa tufafi aiki ne mai cin kuɗi, musamman yadda ake da gasa daga China, yana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta cika alƙawarinta na tallafa wa masu masana’antun gida.
“Zan so in gode wa Shugaban Ƙasa bisa kyakkyawan ƙoƙarinsa na bunƙasa tattalin arziƙi ta hanyar ƙarfafa gwiwar samar da kaya a gida.
“Zan kuma so in gode wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa ƙoƙarinsa na ganin Kano ta dawo da matsayinta na jiha mafi ƙwazo wajen saƙa tufafi”, in ji shi.
Shugaban Kamfanin ya kuma yi kira ga Babban Bankin Najeriya, CBN, da ya sassauta wasu daga cikin manufofinsa don bada damar yin kasuwanci ba tare da tazgaro ba don kuma ci gaban ƙasa.