An Yi Shagalin Bikin Sunan Akuya A Kano

148

An shiryawa wata Akuya mai suna Abida mai shekara daya a duniya ƙasaitaccen bikin suna domin taya ta murnar haihuwar ɗa Namiji a jihar Kano.

Mai Akuyar mai suna Rukayya Muhammad Lawal ‘yar Asalin jihar Zamfara dake zaune a Kano , tace dalilin da yasa ta shiryawa Akuyar tata bikin sunan a yau, ta shafe sama da shekaru ashirin da yin aure kuma ta haifi ‘ya’ya bakwai amma duk sun mutu babu wanda yayi saura hakan yasa ta sayi Akuya da ta yiwa lakabi da suna Abida, kuma Allah ya albarkace ta da haihuwar ɗa namiji ta kuma saka masa suna Murtala a yayin bikin sunan da aka yi a yau

Rukayya Muhammad Lawal ta ƙara da cewa haihuwar da akuyar tata tayi, ya sanya ta matukar farin ciki wanda hakan yasa ta shirya gagarumin suna ta kuma gayyaci mutane daga wurare daban-daban domin su zo su tayata farin ciki , sun kuma yi girke-girke kala daban-daban domin nuna farin ciki da haihuwar akuyar Abida.


Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya halarci taron bikin sunan ya ruwaito cewa a yayin taron sunan an yiwa Akuyar Abida kasaitacciyar kwalliya ta gani ta fada tare ɗan akuyar data haifa mai suna Murtala.

Rahoton Freedom Radio, Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan