Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar wa da ma’aikatan gwamnati a jihar cewa za a biya su ariyas-ariyas na sabon mafi ƙarancin albashi da zarar an fara biya.
Idan dai ba a manta ba, Gwamna Ganduje ya yi alƙawarin biyan N30,600 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a jihar.
Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, Kabiru Shehu ya bada wannan tabbaci a maimakon Gwamna Ganduje a yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Litinin.
“Mun lura cewa Gwamnatin Tarayya ta umarci Ma’aikatar Kuɗi da ta fara biyan ariyas-ariyas daga Afrilu.
“Mun lura da wannan, kuma za mu aiwatar da haka mu ma.
“Mun karɓi waccan shawara kuma da yardar Allah, idan muka zo aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashinmu, za mu lura da biyan ariyas-ariyas, amma da akwai bambanci tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta jiha, saboda haka duk abinda za mu yi, za mu yi shi dai-dai da ƙarfin tattalin arziƙin jiharmu”, in ji shi.
Ya ƙara da cewa har yanzu gwamnati ba ta fara biyan sabon albashin ba saboda tattaunawa da ake ci gaba da yi da ƙungiyoyin ƙwadago kan yadda ƙarin albashin zai kasance ga ma’aikatan dake kan matakin albashi na 7-17.