Golden Eaglets Zasu Fafata Wasansu Na 2 Da Ecuador

103

Kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 17 wato Golden Eaglets zata fafata wasanta na biyu na gasar cin kofin duniya adaren yau Talata da kasar Ecuador.

Wasan farko dai Najeriya ta lallasa kasar Hungry daci 4 da 2 inda ita kuma Ecuador ta caskara kasar Australia daci 2 da 1.

A rukunin na B da Najeriya da Ecuador kowacce nada maki 3.

Ministan wasanni na kasarnan wato Sunday Dare ya bukaci ‘yan wasan na Najeriya dasu dage su lallasa kasar ta Ecuador ayau.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan