Mai Martaba Sarkin Ƙaraye Ya Rushe Majalisar Masarautarsa

204

Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar II ya rushe majalisarsa bayan kammala wata ganawa da duk masu rike da mukamai a masarautar.

Babban ɗan majalisar Sarkin Magajin Garin Karaye Injiniya Shehu Ahmad ne ya sanar da hakan, sai dai ya ce rushewar ba ta shafi wasu Hakimai guda takwas na Masarautar ba.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Karaye Haruna Gunduwawa ya fitar a jiya.

Sanarwar ta kara da cewa Sarkin ya jaddada aniyarsa ta fadada mukaman a cikin kananan hukumomi 8 na Masarautar, tare da alkawarta cewa wasu daga masu rike da mukaman za su dawo yayin da wasu kuma za a daga likkafarsu.


Ya kuma jinjinawa ‘yan majalisar ta sa bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ciyar da masarautar ta karaye gaba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan