Majalisar Dattijai Ta Hana Jami’ar Maiduguri Ƙara Kuɗin Makaranta

187

A ranar Talata ne Majalisar Dattijai ta umarci hukumomin Jami’ar Maiduguri, UniMaid, da su dakatar da shirinsu na ƙara kuɗin makaranta.

Majalisar Dattijan ta kuma umarci Kwamitinta na Manyan Makarantu da ya yi aiki tare da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, wajen fito da tabbataccen tsarin kuɗin makaranta na bai ɗaya a dukkan manyan makarantu.

Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa, Abba Kyari ne ya jawo hankalin abokan aikinsa game da ƙarin kuɗin makarantar a lokacin da ya gabatar da ƙudiri game da haka.

Ya ce ƙarin kuɗin makarantar daga kaso 40 cikin ɗari zuwa kaso 400 cikin ɗari zai tilasta matasa su bar makarantar su kuma zama ‘yan tada ƙayar baya, abinda zai ƙara munana yanayin tsaro a ƙasar nan.

Ya bada misalin kuɗin wata makaranta da da ake biyan N25,000, amma yanzu an ƙara shi zuwa N125,000.

Ya ce ƙarin kuɗin makarantar zai shafi ilimi a Arewa Maso Gabas.

Ya ce tabbatar da makarantu suna buɗe a yanayin zaman lafiya yana da muhimmanci wajen yaƙi da rashin tsaro musamman a Borno.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan