Najeriya Ce Ƙasar Da Mutane Suka Fi Yin Bahaya A Fili- Ministan Ruwa

272

Gwamnatin Tarayya ta ce a halin yanzu Najeriya ce ƙasa ta ɗaya a duniya wadda mutanenta su ka fi yin bahaya a bainar jama’a.

Suleiman Adamu, Ministan Albarkatun Ruwa ya bayyana haka yayinda yake buɗe wani taron bita na kwana biyu Na Kamfanonin Shara Masu Zaman Kansu a ranar Litinin a Abuja.

Haɗaɗdiyar Ƙungiyar Kamfanonin Kwashe Shara Masu Zaman Kansu ita ta shirya taron mai taken: “Tattara Yunƙurin Kamfanonin Shara Masu Zaman Kansu Wajen Kawo Ƙarshen Bahaya A Bainar Jama’a”.

A ranar 2 ga Oktoba, aka cire Indiya a matsayin ƙasar da ke da mafiya yawan mutane da suka fi yin bahaya a bainar jama’a a duniya.

A cewar Mista Adamu, a halin yanzu Najeriya ce a lamba ta ɗaya ta fuskar yawan mutane dake bahaya a bainar jama’a a Afirka.

“Bugu da ƙari, muna gaɓar zama na farko a duniya, saboda a ƙalla mutane miliyan 47 ba su da damar a yadda ya fi kamata daga tushe.

“Abin fahimta, wannan abin damuwa ne ga dukkanmu saboda yana da tasiri mai yawa ga tattalin arziƙi kuma yana hana ci gaban ƙasar nan”, in ji shi.

Ya ce Shirin Ci Gaba Mai Ɗorewa, SDG, yana da manufar tabbatar da cewa an samar da kayayyakin wanke hannu da kuma ta’ammali da ruwa yadda ya kamata nan da 2030.

Ya ce shirye-shiryen SDG, Target 6.2 shi ma yana mayar da hankali wajen samar da tsaftar muhalli ga kuwa da kuma kawo ƙarshen bahaya a bainar jama’a, tare da bada isasshiyar kula ga buƙatun mata da ‘yan mata da waɗanda suke cikin halin matsi.

Ministan ya ce koda yake SDGs sun bayyana waɗannan muradu, sun kuma fito da wasu matsaloli waɗanda za su buƙaci a dunƙule hannu wajen ɗaya don shawo kansu, “wanda shi ne abinda ya dame mu har muka shirya wannan taron bita”.

“Banda jawo cututtuka, akwai rashin kima da yake cikin yin bahaya a bainar jama’a, musamman ta fuskar mata da ‘yan mata. Saboda haka, akwai batun rashin daidaito a jinsi wanda dole a shawo kansa cikin gaggawa.

“Idan ba a samu mafitar da ta dace ba, rashin kayayyaki tsafta yana jawo wa mata da ‘yan mata tashin hankali da ya haɗa da fyaɗe, idan aka tilasta musu su fita waje su yi bahaya.

“Kuma, zan jaddada cewa wannan matsala tana da illoli da yawa ta fuskar faɗin abubuwan take haifarwa.

“A matsayin ɓangaren ƙoƙarin da ake yi na shawo kan batun musamman ta fuskar kawo ƙarshen yin bahaya a bainar jama’a, a shekarar 2006, an ƙirƙiri tare da ƙaddamar da Wani Shirin Ƙasa na Ganin An Daina Bahaya A Bainar Jama’a Daga Nan Zuwa 2025, ODF.

“Amma, nasara kaɗan aka cimma a wajen aiwatar da Shirin na Ƙasa inda aka bayyana ƙananan hukumomi 14 a matsayin waɗanda ba a yin bahaya a cikinsu a bainar jama’a kawo yanzu, a cewar National ODF Protocol.

“Amma, abin sha’awa ne a lura da irin kyawawan ƙoƙarin da maaikatata ta yi a ɓangaren, Ruwa, Tsaftar Muhalli da Kiwon Lafiya, wato WASH a Turance wajen inganta rayuwar al’ummarmu a yankunan birni da karkara.

“Damar samun Ruwa, Tsaftar Muhalli da Kiwon Lafiya, WASH, tana daga cikin abubuwan da ake buƙata wajen ci gaban kowace ƙasa, saboda haka ba za a iya watsi da su ba”, in ji Mista Adamu.

Ministan ya ce amma, ba za a raina irin rawar da kamfanoni masu zaman kansu za su iya takawa ba ta fuskar farfaɗo da ɓangaren WASH, a matsayin wani inji na ci gaban tattalin arziƙi kuma manya-manyan masu ruwa da tsaki wajen ƙirƙirar sabbin abubuwa waɗanda ke samar da kuɗaɗe ga abubuwan da WASH ke samarwa.

Ya ce a tarihi, kamfanoni masu zaman kansu koyaushe su kan taka muhimmiyar rawa wajen zuwa da sabbin fasahohi da warwarewar matsaloli ga ci gaba.

“Amma, wannan shi ne lokaci na farko da aka yi kira wajen cin irin moriyar ikon da kamfanoni masu zaman kansu ke da shi ta hanyar haɗa hannu wuri guda don kawo matsalar ƙarancin WASH a duniya.

“SDGs sun kuma jaddada wannan batu cewa ba za a iya kakkaɓe rashin daidaito a ruwa da tsaftar muhalli ba ba tare da an mayar da hankali ga kamfanoni masu zaman kansu ba”, in ji shi.

Ya ce manufar shirya taron shi ne a fito da wuraren da kamfanoni masu zaman kansu za su shiga a dama da su game da batutuwan WASH, kuma sakamakon haka, su zo da sabbin hanyoyi kan yadda za a yi maganin matsalolin yadda ya dace.

“Wannan taron bitar zai yi maganin matsalolin da ake fuskanta wajen samar da kuɗaɗe ga ɓangaren WASH, ta hanyar haɗa kai da dukkan masu ruwa da tsaki da ya haɗa da kamfanoni masu zaman kansu don cimma buƙatun Shirye-shiryen Ci Gaba Masu Ɗorewa, SDGs, na WASH zuwa 2030”, a kalaman Mista Adamu.

Nicolas Igwe, Manajan Daraktan Zenith Project Ltd ta ce an shirya wannan taron bitar na kwana biyu ne don a fito da irin ƙarfin haɗa hannu wuri guda da kamfanoni masu zaman kansu ke da shi wajen warware matsalolin WASH ta kuma cimma tsarin ƙwarewa a matakin ƙasa da ƙasa.

Mista Igwe ya ce akwai buƙatar ƙarfafa gwiwa don jaddada warware matsaloli ta ɓangare da dama a matsayin al’adar kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya.

Benson Attach, shugaban wata ƙungiya mai rajin kare muhalli mai suna Society for Water, Sanitation and Hygiene, ya ce ƙungiyar a shirye take wajen taimakon Gwamnatin Tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da sauran abokan aiki wajen tunkarar matsalolin WASH a ƙasar nan.

“Muna so mu yi kira ga dukkan abokan aiki don tabbatar da cewa mun kauce wa batutuwan da za su kawo mana ci gaba ba, kuma mu fuskaci matsalolin da za su ba mu damar Samar Da Al’umma Da Ba Ta Bahaya A Bainar Jama’a, ODF, zuwa 2025”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan