Nan Gaba Kaɗan ‘Yan Najeriya Za Su Yaba Wa Buhari Bisa Rufe Boda- Ɗan Majalisa

231

Wani Ɗan Majalisar Dokokin ta Jihar Legas, Victor Akande, ya ce ko badaɗe ko bajima, ‘yan Najeriya za su yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa bakin iyakokin ƙasar nan da ya yi.

Mista Akande, mai wakiltar Mazaɓar Ɗan Majalisar Dokoki ta Ojo I a Majalisar Dokokin Jihar Legas, ya bayyana haka ne yayinda wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ranar Talata a Legas.

Ɗan Majalisar, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar na Alƙalai, Haƙkin Bil’adama, Ƙorafe-Ƙorafe da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Legas, LASIEC, ya ce rufe bodar yana da alfanu ta ɓangaren tsaro da tattalin arziƙi.

Mista Akande ya ce: “Amfanin rufe bodarmu ya fi rashin amfanin yawa a halin yanzu.

“Ba lallai ‘yan Najeriya su fahimci haka ba a yanzu, wata ƙila saboda ɗan raɗadin da ake ji, amma tasirin da zai biyo baya zai sa ‘yan Najeriya su yaba wa Shugaba Ƙasa bisa yin haka.

“Tsaron ƙasarmu babban abu ne kuma wanda ya dace; idan ba a ɗauki wannan mataki ba yanzu, zai yi wahala a iya shawo kan zirga-zirgar mutane, makamai da albarusai dake shigowa ƙasar nan, balle kuma mu yi nasarar yaƙi da tada ƙayar baya”, in ji shi.

Ɗan Majalisar ya roƙi ‘yan Najeriya da su yi haƙuri da gwamnati, yana mai cewa ci gaba da rufe bakin iyakokin shi ne abinda ya fi alheri ga tattalin arziƙi da tsaron ƙasar nan.

“Muna buƙatar rufe bodar don yaƙar rashin aikin yi a ƙasar nan. Sha’awarmu ta son yin amfani da kayayyakin ƙasashen waje cutar da mu take yi.

“Mukan sama wa ‘yan ƙasashen da ake shigo da waɗannan kayayyaki daga gare su aiki, yayinda matasanmu ba su da aikin da za su yi.

“Matuƙar ba a amfani da kayanmu na gida, mun yanke hukuncin kisa ga damammakin samun aikin yi a ƙasarmu.

“Rude bodar zai sa mu yi duba zuwa cikin ƙasarmu muka abinda za mu iya yi wa kanmu, mu ma koma noma. ‘yan Najeriya za su yaba wa gwamnati nan da wani lokaci”, in ji Mista Akande.

A ta bakinsa, rufe bodar zai ɗora ƙasar nan a kan turbar ci gaba ta tattalin arziƙi da kuma samun ci gaba ta hanyar farfaɗo da masana’antun gida.

“Za mu kasance mun kai matakin iya ciyar da kai. Dama ce gare mu mu ci gaba. A halin yanzu, mutane suna ta girbi da samar da shinkafa a ko’ina, wanda abu ne mai kyau a gare mu”, in ji Ɗan Majalisar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan