Ra’ayi: A Bar Kowa Ya Yi Addininsa Ba Tare Da Tsangwama Ba

244

A Najeriya, mutum yana da ra’ayi ya shiga duk addinin da ya ga dama wanda yake ji ya yi masa a ransa ba tare da nuna banbanci ko tsangwama ba.

Wannan shi ne dalilin da yasa Najeriya ta zama ‘Secular State’, ma’ana ƙasar da ba ta bin wani tsarin addini, a matsayin addininta. Shiyasa aka samu dai-daito ta wajan tsarin tafiyar da ƙasa domin wanzar da zaman lafia a tsakanin ‘yan ƙasa.

Duba da Najeriya tana da mabiya addini daban-daban, addinin Musulumci yana da tsarin dokokinsa da mabiya suke bi haka addinin Kirista shi ma yana da nasa tanadin da mabiyansa sukebi.

Tunda ƙasar ba ta ɗauki wani addinta ba a matsayin wanda za ta bi, sai aka haɗu a Tsarin Mulki, (Constitution), amma shi Kundin Tsarin Mulkin da ake magana akwai shafin da ya yi dogon bayani a kan Haƙƙin Ɗan Adam, gwari-gwari mu ce Human Right, a ƙarƙashin ‘yancin ɗan Adam akwai wasu damarmaki da ya bada, nas shiga inda ka ke so, faɗin albarkacin baki, shiga duk addinin da ya yi maka, da kuma kare haƙƙin ɗan Adam ɗin da ake magana.

In kuwa kowa yana da damar da zai shiga inda yake so ko addini ko cikin ƙasa ko wajan ƙasa ban ga dalilin da zai sa a kama Yunusa Yellow ba kawai dan mace ta musulunta a hannunsa tunda ai tana da damar da za ta zabi abinda take so. Kuma ban ga inda Kundin Tsarin Mulki ya ce a tsare mutum ba saboda wannan, ka ga kenan ƙarara an saba wa shi Kundin Tsarin Mulkin da ake kansa. Saboda haka Gwamanatin Bayalsa, ta saɓa wa Dokar Haƙƙin Ɗan Adam (Human Rights Act).

Daga Shu’aibu Lawan

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan