‘Yan Najeriya Miliyan 90 Na Rayuwa Cikin Talauci- Sadiya Farouq

244

Sadiya Umar Farouq, Ministar Ayyukan Jin Ƙai, Kare Afkuwar Annoba Da Walwalar Jama’a, ta bayyana shirin Gwamnatin Tarayya na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 90 da a halin yanzu suke rayuwa a cikin talauci a faɗin ƙasar nan.

Misis Farouq ta bayyana haka ne yayinda take kare kasafin kuɗin ma’aikatarta 2020 na Naira Biliyan N44.21 a gaban Kwamitin Waɗanda Rikicin Cikin Gida Ya Raba da Muhallinsu Da ‘Yan Gudun Hijira na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, wanda Ɗan Majalisa Mohammed Jega ya jagoranta.

Ministar ta ce an ɗora wa Ma’aikatar Ayyukan Jin Ƙai, Kare Afkuwar Annoba Da Walwalar Jama’a nauyin shawo kan wasu dalilan dake haifar da rikici tsakanin al’umma da kuma illar da suke haifarwa haɗi da koma baya.

Ta ce wannan ya haɗa da yadda kusan rabin al’ummar ƙasar nan (miliyan 90) daga cikin milyan 198 ke rayuwa cikin talauci.

Ministar ta ce sabuwar ma’aikatar za ta ƙarfafa aikin haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen kare rikice-rikice tsakanin al’umma da kuma kare afkuwar annoba.

Kasafin kuɗin ya ƙunshi tanadin N474,306,285 ga Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Baƙin Haure da Waɗanda Rikicin Cikin Gida Ya Raba da Muhallinsu, don kula da ma’aikata, Miliyan N165 don sake tsugunar da ‘yan gudun hijira, IDPs a Arewa Maso Gabas da ‘yan gudun hijirar Bakassi a kasafin kuɗin na 2020.

Sauran su ne Miliyan N15 don a shigar da IDPs 1000 cikin Tsarin Inshorar Lafiya na Ƙasa, NHIS; Miliyan N60 don biyan kuɗaɗen komawa makaranta; Miliyan N105 don haƙa fanfunan burtsatse, Miliyan N184 don samun filin da za a dawo da IDPs a Abuja da jihar Nasarawa, sai kuma Miliyan N110 don biyan tallafin dawowa ga iyalai 2,200 a Arewa Maso Gabas da sauransu.

Da yake jawabi, Shugaban Kwamitin ya tabbatar da cewa kasafin kuɗin zai yi tasiri ga rayuwar dukkan ‘yan Najeriya.

“Saboda haka muna kira da a samu haɗin kai daga Ɓangaren Zartarwa don tabbatar da cewa mun yi kasafin kuɗi mai aiki da zai biya buƙatun ɗimbin al’umma”, in ji shi.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin Shugaba Muhammadu Buhari bisa ƙirƙirar sabuwar ma’aikatar da nufin magance matsalolin ayyukan jin ƙai a ƙasar nan sakamakon rikicin tada ƙayar baya, rikicin mahara da sauran rikice-rikice.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Mata na Majalisar Wakilai, Ɗan Majalisa Oriyomi Onanuga, ya yi alƙawarin shawo kan matsalar rashin aikin yi (kaso 23.2 cikin ɗari), inda fiye da matasa miliyan 40 ba su da aikin yi ko kuma suna yin ayyukan da ba sa biyan buƙatunsu.

Mista Onanuga ya kuma yaba da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na warware matsalar yawan mutanen da ba su da aikin yi haɗa da fiye da IDPs miliyan biyu, ‘yan Najeriya 230,000 dake zaune a Nijar, Cadi da Kamaru da kuma ‘yan gudun hijira a Najeriya kimanin 45000.

“Wannan ya haɗa da mutane masu buƙata ta musamman miliyan 22; fiye da mutane miliyan 14 masu shan muggan ƙwayoyi da kuma ƙaruwar tsofaffi da gajiyayyu”, a kalaman nasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan