An Cafke Matar Da Ta Ƙware Wajen Fataucin ‘Yan Mata Don Karuwanci

55

Rundunar Seme ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, NIS, ta ce ta cafke matar da take zargi da safarar ɗan Adam da kuma shigo da kaya ba bisa ƙa’ida ba a bakin Iyakar Najeriya da Benin a garin Seme.

Kwanturola Janar na Rundunar, Joshua Ajisafe ya bayyana haka ranar Laraba a Legas.

Mista Ajisafe ya ce matar da ake zargin ta ƙware wajen yaudarar ƙananan yara mata da alƙawarin sama musu ayyuka masu tsoka a Jamhoriyar Benin.

Ya ce matar da ake zargin tana ɗaukar waɗannan yara ta sa su karuwanci da kuma lalata ta hanyar bautarwa.

“A ranar 16 ga Oktoba, jami’anmu a Seme suka cafke ‘yan mata ƙanana guda uku (an ɓoye sunayensu) ‘yan jihar Kaduna.

“Da muka tambaye su, mun gano ‘yan mata ne ‘yan Najeriya, waɗanda suka faɗa tarkon fataucin ɗan Adam.

“Sun yi sa’ar tsira daga hannun waddda ke riƙe da su, suna ƙoƙarin ƙetara boda don dawowa gidajensu a Najeriya.

“An gano cewa wadda ake zargi da simogar da aka kama ta ɗauke su cikin yaudara daga Najeriya zuwa Kwatano don yin kasuwanci”, in ji Mista Ajisafe.

Ya ce duk lokacin da ‘yan matan da matar da ake zargi ta sace suka yi yunƙurin tserewa, sai ta jibga musu bashin da ba za su iya biya ba.

“Da zarar wata daga cikinsu ta yi yunƙurin guduwa don aurar waɗanda ke lalata da su a asirce ko kai rahoto ga jami’an tsaro, sai ta aske musu gashin mara, faratansu, gashin hammata ta kuma barazanar haukatar da su.

“Waɗannan ‘yan mata, ba don suna so ba, suke yadda su shiga karuwanci da kuma lalata ta hanyar bautarwa.

“Sai matar ta yi musu alƙawarin za ta ‘yanta su bayan kowace ɗaya cikinsu ta biya ta maƙudan kuɗaɗe ta hanyar sana’ar karuwancin”, in ji kwanturolan.

Ya ce ‘yan matan sun iya tserewa daga ɗakunan otel ɗin da aka ajiye su lokacin da matar da ake zargin ta dawo Najeriya don ta ƙara yaudarar wasu ‘yan matan don safara.

“Tawagar jami’anmu na sirri suka zabura, sannan suka yi dukkan binciken da ya wajaba don cafke matar da ake zargin.

“A aikin haɗin gwiwa da jami’an ‘yan sanda a Benin, a cikin kwanaki biyar, mun iya kama matar da ake zargin wadda ta shigar da ‘yan matan Najeriya da yawa karuwanci a wani otel a Jamhoriyar Benin”, in ji shi.

Kwanturola Janar ɗin ya ce tuni an miƙa matar da ake zargin ga Hukumar Hana Fataucin Ɗan Adam ta Ƙasa, NAPTIP, don ɗaukar matakan da suka wajaba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan