Besiktas Zasu Dawo Da Karius Liverpool

121

Kungiyar kwallon kafa ta Besiktas dake kasar Turkey ta bayyana cewar zata hakura da mai tsaron gidan data karba a hannun kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wanda ta karba amatsayin aro.

Domin kungiyar tace kawai hakuri sukeyi dashi domin kuwa yakaiku Bango.

Karius dai idan ba a manta ba dalilin kaishi aro kungiyar kwallon kafa ta Besiktas shine tun cin da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tayiwa Liverpool awasan karshe na gasar zakarun nahiyar turai inda ake ganin cewar laifinsane kwallayen da akaci Liverpool musamman cin Benzema na farko da kuma kwallon Bale ta karshe duk laifin sane.

To hakan ma tana ta faruwa a kungiyar kwallon kafan ta Besiktas shiyasa sukace sufa zasu dawo da wannan dan wasa a watan Janairu domin sun gaji dashi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan