Kotun Ƙoli Ta Yi Watsi Da Ƙarar Atiku

142

A ranar Laraba ne Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar PDP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar su ka shigar gabanta inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 23 ga Fabrairu.

Gungun alƙlalai bakwai na Kotun Ƙolin ƙarƙashin jagorancin Alƙalin Alƙalan Najeriya, CJN, Tanko Mohammed suka ce sun kori ƙarar ta PDP da Atiku ne bisa rashin cancancta.

CJN ɗin ya ƙara da cewa alƙalan sun yi bitar ƙarar tsawon makonni biyu da suka gabata.

Ya ce a nan gaba ne za a bada dalilan da suka sa aka yi watsi da ƙarar.

Atiku da jam’iyyarsa suna ƙalubalantar hukuncin 11 ga Satumba na Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa wadda Mai Shari’a Mohammed Garba ya jagoranta, wadda ta tabbatar da nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen na 23 ga Fabrairu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan