Mun Ƙwace Kayyaki Da Kuɗinsu Ya Kai Biliyan 2.713- Hameed Ali

56

A ranar Talata ne Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS, ta ce ta ƙwace kwantainonin shinkafa, ƙwayar tiramadol da magunguna marasa rijista da kuɗisu su ka kai N2,713,865,051.

Kwanturola Janar na Hukumar, CG, Hameed Ali, ya bada wannan alƙaluma a yayin gabatar da kayyakin da su ka ƙwace a Legas.

Ya ce ƙwace kayayyakin yana ɗaya daga cikin nasararorin rufe bakin iyakokin ƙasar na wucin gadi da aka yi.

A ta bakinsa, ƙwacen kayan, wadda Rundunar Tsibirin TinCan ta NCS, TinCan Island Port Command ta jagoranta, ya haɗa da kwantenonin shinkafa 33, kwntenar shinkafa ɗaya wadda aka rufe ta da kayan gyara da kuma kwantenoni 11 na magunguna marasa rijista.

Mista Ali, tsohon kanar ɗin soja mai ritaya, ya ce ƙwace kayan ya kuma haɗa da kwantenoni biyu na tsofaffin tayoyi, kwantena ɗaya ta tsofaffin tufafi da kwantenoni huɗu na man girki.

CG ɗin ya ce jimillar kwantenonin sun kai 54, da suka haɗa da 15 by 40-feet da 39 by 20-feet.

Ya ce dukkan ƙwacen yana cikin tanadin Dokar Gudanar da Aiki ta Hukumar Hana Fasa Ƙwauri.

Ya yaba wa jami’an TinCan Island Port Command bisa karɓar kuɗaɗen shiga da su ka kai N286,742,551,443 tun daga watan Janairu.

“Abu ne da kowa ya sani cewa Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa tana jagorantar sauran hukumomin tsaro wajen aikin haɗin gwiwa da aka sa wa suna ‘Ex Swift Response’ wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro ke kula da shi.

“NCS, Hukumar Kula da Shige da Fice, da haɗin guiwar Rundunar Sojin Najeriya, Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa da jami’an Hukumomin Tsaro na Sirri suna nan suna tabbatar da rufe bakin iyakokin ƙasar nan da aka yi na wucin gadi.

“Tunda aka fara aikin, an ƙwace kayayyaki masu ɗimbin yawa a duk faɗin yankuna daban-daban da muke aiki.

“Kuma abu ne da aka sani cewa rufe bodar da aka yi na wucin gadi ya taimaka wajen dawo da jiragenmu na ɗaukar kaya zuwa tekuna, kuma wannan ya bada damar ƙwace ɗimbin kaya, waɗanda ba don haka ba da tuni an shigo da su ta bakin iyakokin ba bisa ƙa’ida ba”, in ji shi.

Mista Ali ya ce buhunan shinkafar da aka ƙwace ko dai sun lalace ko kuma sun kusa lalacewa.

“Hukumar ta faɗakar ta kuma jawo hankalin al’umma zuwa ga gaskiyar cewa da yawa daga cikin shinkafar da aka shigo da ita lalatacciya ce.

“Haka kuma, tun a baya, hukumar ta fito da haɗarin amfani da ƙwayar tiramadol ta kuma ƙwace tare da fara lalata tiramadol da kuɗinta ya kai Biliyan N14 kwanan nan.

“Abin kaico ne cewa waɗanda ke shigo da waɗannan kaya masu haɗari ba sa nufin mu da alheri. Yi tunani abinda zai faru da a ce sun yi nasarar shigo da lalatacciyar shinkafar, sake mata buhu, su kuma canza mata kwanan watan lalacewa don ‘yan Najeriya su ci.

“Za a iya tunanin mummunan tasirin da cin wannan shinkafa zai iya yi, kafin a iya ji a jiki.

“Don a guje wa shakka, bari in nanata ƙoƙarin NCS da sauran hukumomi ‘yan uwanta na tsare bakin iyakokinmu na ƙasa daga waɗannan kaya masu haɗari. Wannan gargaɗi ne ga dukkan mashigar ruwa da mafitar ruwa a Najeriya”, in ji shi.

Mista Ali ya ce tuni ya bada umarni a yi cikakken bincike don gurfanar da dukkan waɗanda ke da dangantaka da shigo da kayayyakin gaban shari’a.

Magungunan da aka kama sun haɗa da chloroquine phosphate 20mg tabs, Hyergra 120, Artesam, Vitamin B complex injection, Comefwn Forte da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan