Sama Da Mata Ƴan Makaranta 7,000 Ne Su Ka Yi Cikin Shege A Ƙasar Ghana

383

Matsalar daukar juna biyu na kananan yara mata na neman zama ruwan dare a wasu sassan kasar Ghana.

Yanzu haka hukumar kula da ilimi ta kasar ta ce an samu kananan yara mata 7,239 na makarantun firamare da karamar sakandire da suka samu ciki a shekara ta 2018 zuwa 2019 a fadin kasar baki daya.

Bayanai na nuna cewa mata dalibai yan shekaru goma zuwa sama suna yawan samun juna-biyu, inda a wasu lokuta lamarin yake kawo karshen karatunsu.

A cewar hukumomi matsalar yawan daukar cikin yaran mata ya kai kaso 14.2, wanda hakan wata babbar matsala ce ga gwamnati.

Wata mai fafutikar kare hakkin mata a Ghana, Hajara Inna dikko ta ce talauci na daga cikin abubuwan da ke haddasa daukan cikin ga yara mata a kasar.

“Yaran da suka fito gidan marasa kudi, ba su samun kulawa, idan suka samu wani yana ba su kudi, sai ya yi amfani da wannan dama ya yi masu ciki.”

Sai dai Hajara Inna ta ce za a iya shawo kan matsalar ta hanyar koya wa yara ilimin jima’i

A yanzu dai hukumomi sun fara fadakarwa kan yadda za`a tallafa wa yaran da ke fadawa cikin wannan hali domin su ci gaba da karatu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan