Yadda Za A Magance Yaɗa Kalaman Ɓatanci, Labaran Ƙage- Lai Mohammed

162

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bada shawara a ƙara tarar da ake cin kafafen watsa labarai masu karya doka ta hanyar yaɗa kalaman ɓatanci, kalaman tunzuri da baɗala daga N500,000 zuwa N5,000,000.

Ministan, wanda ya bada wannan shawara a wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, ya ce ce wannan mataki ya yi dai-dai da Shirin Yaƙi da Labaran Ƙage da Kalaman Ɓatanci na Ƙasa da aka ƙaddamar a watan Yuli da ya gabata.

Mista Mohammed ya ce: “A cikin wancan shiri, kwanan na ƙaddamar da wani yunƙuri don raba gidajenmu na rediyo da talabijin da labaran ƙage da kalaman ɓatanci.

“A taƙaice, na kafa wani kwamiti wanda zai aiwatar da shawarwarin waɗanda Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da su don samar da tsafta a gidajen rediyo da talabijin na ƙasar nan, biyo bayan rashin ƙwarewa da rashin ɗa’a na wasu gidajen rediyo da talabijin, musamman kafin da bayan zaɓukan da suka gabata”.

A ta bakinsa, wasu daga cikin shawarwarin da ya bayar sun haɗa da samun ‘yancin Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin, NBC daga tsoma bakin ‘yan siyasa a wajen gudanar da ayyukanta da doka ta ɗora mata, musamman wajen bada ko karɓe lasisin watsa labarai.

Sauran su ne ƙara duba Dokar Yaɗa Labara ta Ƙasa, NBC, da dokokin yaɗa labarai da ake aiki da su a halin yanzu don yin gyare-gyare kamar haka; duk wata kafar yaɗa labarai da ta maimaita karya doka har sau uku bayan an ci tatar ta za a ƙwace lasisinta.

Ministan ya ƙara da cewa an ɗaga darajar ra’ayoyin siyasa masu alaƙa da kalaman ɓatanci da kalaman raba kan jama’a zuwa laifukan “Ajin A” a Dokar Watsa Labarai, da kuma gyara Dokar ta NBC don ta iya bada lasisi ga gidajen talabijin da rediyo na Intanet.

Mista Mohammed ya ce dole a ɗauki ƙarin ma’aikatan sa ido ga NBC, kamar yadda ya ce a halin yanzu, akwai ma’aikatan sa ido 200 ne kawai da suke kula da gidajen rediyo da talabijin kimanin 1,000.

Ya kamata a samu “tura isassun kayan aikin sa ido da fasaha ga NBC kuma a bunƙasa shirye-shirye na jin daɗin ma’aikatan NBC don kada su kauce hanya a yayin da suke kan aiki”, in ji ministan.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan