2023: An Buɗe Ofishin Takarar Shugaban Ƙasa na El-Rufa’i A Filato

230

Nasiriyya Organisation Support Group, NOSG, wata ƙungiya siyasa da take iƙirarin goyon bayan Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna don yin takarar shugaban ƙasa a 2023, ta buɗe ofishin kamfe a Jos, jihar Filato.

Yayinda yake ƙaddamar da mambobin zartarwa na ƙungiyar, da kuma ofishin ƙungiyar a Jos, shugaban NOSG na ƙasa, Ibrahim Garkuwan-Rijau, ya ce sun yanke shawarar fara saka tubala a dukkan faɗin Najeriya don ba su damar cimma nasara a tafiyarsu.

“A Arewa, ba mu fara da wuri ba. Idan a Legas mutane sun fara kira da goyon bayan Malam Nasiru El-Rufa’i ya yi takara, me yasa ba za mu yi haka a nan ba?,” ya yi tambaya.

Mista Garkuwan-Rijau, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC a Arewa Maso Yamma, ya ce iya tafiyar da mulki na Gwamna El-Rufa’i da dabarunsa na siyasa sun isa a goyi bayan buƙatarsa don zaman shugaban ƙasar Najeriya na gaba.

A ta bakinsa, Gwamna El-Rufa’i shi ne irin shugaban da Najeriya ke son samu a 2023, yana mai ƙarawa da cewa wannan ƙungiya ta dukkan ‘yan Najeriya ce, ba tare da lura da bambancin jam’iyya ba.

Ita ma da take jawabi, shugabar ƙungiyar ta jihar Filato, Nafisatu Omar, ta siffanta Gwamna El-Rufa’i a matsayin mutumin da ba ya nuna bambancin ƙabila ko addini, wanda ya dace da aikin Najeriya mai lamba ta ɗaya.

“Malam Nasiru El-Rufa’i shi ne mutum mafi dacewa ga Najeriya a 2023 saboda ba ya cin hanci, ba mai nuna bambancin addini ba ne, ba mai nuna bambancin ƙabila ba kamar yadda ake gani a shugabancinsa a jihar Kaduna, yana rungumar kowa”, in ji ta.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan