Akwai Alkhairi Mai Yawa A Game Da Rufe Iyakokin Ƙasar Nan – Shugaban Muryar Talaka

194

Shugaban ƙungiyar Muryar Talaka na ƙasa reshen jihar Kano kwamaret Balarabe Yusif Babale Gajida, yace hakika rufe iyakokin ƙasar nan yana da matuƙar alfanu mai tarin yawa wajen farfado da tattalin arzikin ƙasar nan tare da samar da tsaro mai ɗorewa.

Kwamared Gajida yace rufe iyakar ƙasar nan na nufin hana shigo da kayan da aka ƙera a wata kasa zuwa cikin ƙasar nan, domin al’ummar ƙasar hakan ne zai ba su ƙwarin gwiwar dogaro da kan mu.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu a Kano akan alfanun rufe iyakokin ƙasar nan, ya ƙara da cewa idan mu ka duba zamu ga mafi yawan abubuwan da muke amfani dasu a cikin ƙasar nan ana shigo da su ne daga wasu ƙasashen ketare ciki har da waɗanda zamu iya samarwa a cikin ƙasar nan, musamman kayan abinci da Allah ya yi mana arziƙin ƙasar noma a arewacin ƙasar nan in da kusan duk abinda ake nomawa a duniya idan aka shuka shi a arewa zai yi.

“Idan har gwamnatin tarayya ba ta rufe iyakar ƙasar nan ba, masana’antun mu ba za su iya gogayya da masana’antu ƙasashen waje ba, domin shigo da kaya daga ƙasashen ketare na ƙara dakushe masana’antunmu na cikin gida tare da ƙara ta’azzara rashin aikinyi a faɗin ƙasar nan” in ji Balarabe Gajida.

Ya ƙara da cewa rufe iyakar ƙasar nan da shugaban ƙasa ya yi ya hana shigowa da gurɓatattun kayayyaki da kuma irin miyagun ƙwayoyin da su kan cutar da lafiyar ɗan’adam.

“Najeriya ta zama bolar kasashen duniya, domim nan ake kawo gurɓatattun kaya ko tsofaffin kaya, wato Dumping Ground a turance, kuma hakan ba abin da zai haifar ƙasar nan ɗa mai ido ba”

A ƙarshe ya bukaci al’ummar ƙasar nan musamman talakawa da su cigaba da yiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari addu’a tare da ba shi goyon baya akan wannan hangen nesan da ya yi na rufe iyakokin ƙasar nan, domin hakan zai farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan