Hukumar Hizba Ta Kano Ta Cafke Mata Masu Zaman Kansu 93

55

Hukumar Hizba ta Jihar Kano ta ce ta cafke mata 93 waɗanda take zargin masu zaman kansu ne, 23 daga cikinsu suna da Ƙwayar Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki, wato HIV.

Kwamandan Hukumar, Sheikh Muhammad Ibn-Sina ya bayyana haka ga manema labarai ranar Alhamis.

Ya ce hukumar ta yi dirar mikiya ne a mararrabar Badume dake ƙaramar hukumar Bichi ta jihar, wanda wuri ne da ya yi ƙaurin suna wajen karuwanci da sauran laifuka.

“Daga cikin adadin da aka kama, likita ya gwada mata 23 da maza huɗu, an samu suna ɗauke da Ƙwayar Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki, HIV”, in ji Mista Ibn-Sina.

Ya ce an gudanar da wannan aiki ne don a tsaftace jihar kamar yadda dokar Shari’ar Muslunci da jihar ke amfani da ita ta hana karuwanci da sauran muggan laifuka.

Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da yaƙi da duk wata irin baɗala a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan