Batun rufe iyakokin Najeriya dai yakasance guda daga cikin manyan batutuwan da suka dauki hankali matuka. Yayin da wasu ke sukar matakin, da yawa daga cikin manazarta na ganin yunkurin a matsayin wani babban abin yabo da za’ace gwamnatin APC tayi tun bayan darewar ta mulki a shekarar 2015.
Daga cikin hujjoji da masu sukar matakin rufe iyakokin kanyi, akwai batun salwuntar da ayyukan yi na mutanen da ke safara tsakanin Najeriya da makwabtan kasashe, matsananci hali da wasu ke ganin talakawan wannan kasa zasu sake tsunduma sakamakon tashin farshin kayayyakin masarufi, sai kuma durkushewar kasuwancin dake da alaka wadannan iyakoki.
Koma dai menene alamu sun nuna wannan mataki bai yiwa wasu ‘yan Najeriya kai harma da makwabtan kasashe dadi ba, to amma abin tambayar shine ko akwa ribar da Najeriya zata iya samu sakamakon daukar wannan mataki?
TA FUSKAR TATTALIN ARZIKI
A sanarwar da hukumar kididdiga ta fidda a tsakiyar wannan shekara ta 2019, adadin mutanen wannan kasa ya haura miliyan 200 wanda a ciki kusan sama da kashi 60 cikin 100 matasa ne dake da karancin ilimi tare da fama da rashin ayyukan yi.
Haka na alkalumma daga babban bankin Najeriya sun nuna cewa a shekara ta 2015 kawai Najeriya na safarar kayayyakin abinci da suka hada da shinkafa, sikari, madara, nama, fulawa, taliya kai harma da tsinken sakucen hakora da dangogin su, wadanda kimar su takai dalar Amurka biliyan 7 da miliyan dari tara ($7.9bn). Kusan kimanin naira tiriliyan biyu da miliyan dari takwas kenan. Kenan a kowacce rana Najeriya na kashe sama da naira biliyan bakwai wajen safarar abinci.
A zamanance babbar gazawa ce ga kasa ace ta kasa rike kanta ta fuskar abinci. Haka na wadancan makudan kudade na zurarewa ne daga lalitar Najeriya zuwa na kasashen da muke sayen kayayyakin daga gare su. Wannan yasa suna samu isassun kudade dake basu damar bunkasa noma da masana’antun su daidai lokacin da namu ke cigaba da durkushewa sakamakon rashin kasuwa.
Garkame iyakoki da gwamnati tayi ya tilastawa ‘yan Najeriya shiga taitayin su ta hanyar fadawa harkokin noma gadan-gadan tare da samar da masana’antun cikin gida. Wannan ya haifar da miliyoyin guraban ayyukan yi ga matasa, karin samun kudade ga gwamnati, rage dogaro da man fetur, dogaro da kai ta fuskar abinci, habaka tattalin arzikin cikin gida ta hanyar kewayar kudade a tsakankanin ‘yan Najeriya, tare da daga likafar tattalin arzikin Najeriya zuwa mataki na gaba.
Kawu Sule Rano, Malami Ne A Sashen Nazarin Halayyar Ɗan Adam Da Ke Jami’ar Bayero A Kano