Home / Wasanni / Arsenal da Juventus Da Manchester City

Arsenal da Juventus Da Manchester City

Kungiyoyin kwallon kafan Arsenal da Juventus da kuma Manchester City dukkaninsu sun rikice akan neman dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wato Isco.

Ita daman kungiyar kwallon kafa ta Manchester City tuni suke neman wannan dan wasa domin duba yaya za ayi ya mayemusu gurbin David Silva dayake shirin barin kungiyar kwallon kafan ta Manchester City.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Juventus tuni take neman wannan dan wasa wato Isco.

Amma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal itace dai sai a ‘yan kwanakinnan tafara neman wannan dan wasa.

Ko wacce kungiyar kwallon kafa ce zatayi nasarar daukan dan wasa acikin kungiyoyin kwallon kafan nan gida uku?

Ita dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana cewar duk kungiyar dake son daukan wannan dan wasa saita biya kudi £m60.3.

About Suraj Naiya Kudiddifawa

Check Also

Aubameyang ya kamu da cutar Maleria

Sai dai Har ya zuwa yanzu Arteta bai iya ba da sanarwar ranar dawowar ɗan wasan gaban ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *