A ranar Juma’a ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Ƙiru/Bebeji a jihar Kano, sannan ta bada umarnin a gudanar da sabon zaɓe.
Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta soke zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomin biyu ne bisa hujjar cewa an yaga sakamakon ƙarshe na zaɓen dake Form EC (8).
A hukuncin, wanda Mai Shari’a Ajoke Adepoju ya gabatar, ya ce tunda an riga an yaga sakamakon, duk wani zato da za a yi bisa haƙiƙanin sakamakon zaɓen jita-jita ne kawai.
A ranar 12 ga Satumba, Kotun Sauraron Ƙorafen-Ƙorafen Zaɓe ta tabbatar da zaɓen Mista Jibrin na jami’yyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Mazaɓar Tarayya ta Ƙiru/Bebeji a jihar Kano a zaɓen 23 ga Fabrairu, 2019.
A wani hukunci da gaba ɗaya alƙalan kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nayai Aganaba suka amince da shi, sun yi watsi da ƙarar da Aliyu Datti Yako na jami’yyar PDP ya shigar gabanta, inda yake ƙalubalantar nasarar da Mista Jibrin ya samu a zaɓen.
Kotun ta tabbatar da cewa masu ƙarar sun kasa kafa hujjojin da za su gaskgata iƙirarinsu a kan waɗanda suke ƙara.
Mista Yako da jami’yyarsa, PDP, sun maka Mista Jibrin a kotu da jami’yyarsa, APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, inda suke ƙalubalantar sakamakon zaɓen Mazaɓar Tarayya ta Ƙiru/Bebeji bisa zargin cewa ba a bi ƙa’idoji ba.
Mista Yako ya yi zargin cewa INEC ta yi kuskure da ta ayyana Mista Jibrin a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’a 41,700 bayan kuma ƙuri’a 40,385 ya samu.
[…] Muƙalar Da Ta GabataKotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Zaɓen Abdulmumin Jibrin Kofa […]