Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars zata bude wasanta na farko a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata sabuwar kakar wasanni ta 2019 zuwa 2020 batare da ‘yan kallo ba.
Hakan ya biyo bayan abin daya faru a wasan ‘yan shida na kakar wasan data gabata ba tsakanin Kano Pillars da Enugu Rangers inda aka tashi wasa 1 da 1.

Inda aka sami magoya bayan kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars da laifin shiga filin wasa.
Yayin tattaunawa da jami’in yada labarai na Kano Pillars wato Rilwanu Idris Malikawa Garu ya tabbatar da kafar yada labarai ta Labarai24 da Wasa.ng cewa tabbas Kano Pillars zata buga wasanni 3 a gida batare da ‘yan Kallo ba sannan kuma andakatar da Rabiu Ali Pele wasu wasanni.
Saidai Malikawa yace hukumar gudanarwar ta Kano Pillars sun nemi da ayimusu sasaauci abisa wadannan hukuncin domin arage adadin yawan wasannin da akace zasuyi babu ‘yan kallo.

Ayanzu dai ta tabbata cewa idan har ba ayiwa Kano Pillars sasaauci ba to zata buga wasannin Rivers Unitedd da Lobi Stars da kuma na Wikki Tourist duk batare da’yan kallo ba.
Agobe dai a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata da misalin karfe 4:00 za a fafata tsakanin Kano Pillars da Rivers United.
[…] Muƙalar Da Ta GabataKano Pillars Zata Buga Wasanta Babu ‘Yan Kallo […]