Katsina United Sun Shirya Tsaf Inji Shugaban Kungiyar Wato Prince

193

Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United wadanda ake kira da Canji Boys sun shirya tsaf domin tunkarar sabuwar kakar wasa ta bana daza a fara a karshen makonnan.

Hakan ma yasa tun a jiya Juma’a da misalin karfe 3:00 na yamma suka dira a Umahia babban birnin jahar Abia inda zasu kara wasan farko tsakaninsu da Abia Warriors.

Shugaban wannan kungiyar kwallon kafa ta Katsina United wato Prince Abdussamad Badamasi yayin tattaunawa da kafofin yada labarai na Labarai24 da Wasa.ng ya bayyana cewar kafin ‘yan wasan na Katsina United subar Katsina kowanne dan wasa saida aka biyashi albashinsa cas.

Prince yakara da cewar burin kungiyar kwallon kafa ta Katsina United shine suga sun lashe gasar ajin Premier ta kasar nan.

Yayin tattaunawa dashi yakara shaidawa kafafen yada labarai na Kamfanin Labarai24 da Wasa.ng cewa ” Nan gaba akwai kudin garabasa na yin nasara a waje kokuma rike kunnen doki nan ma akwai kudin garabasa, haka muna tunanin koda wasa zamuyi a gida akwai kyaututtuka ga masu jefa kwallaye damasu taimakawa aci kwallaye”

Prince Abdussamad Badamasi kai tsaye yace Katsina United sun tafi Umahia domin karbar maki 3 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors.

Awasan mako na biyu kuwa kungiyar kwallon kafan ta Katsina United zata barje gumi da kungiyar kwallon kafa ta Enyimba wato zakarun gasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan