Katsina United Sunyi Garanbawul Domin Lashe Gasar NPFL

203

Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United tayi gyare gyare a kungiyar domin tunkarar sabuwar kakar wasa ta bana daza a fara ta 2019 zuwa 2020 a karshen makonnan.

Ganin hakanne ma yasa kungiyar kwallon kafan ta Katsina United ta sayo ‘yan wasa daga kungiyoyin kwallon kafa daban daban a kasar nan inda harma da dan wasan da aka sayo daga kasar Niger.

Haka kungiyar kwallon kafan dai har sabon mai horas wa ta sauya dama shugaban kungiyar domin cimma gaci.

Kungiayar kwallon kafan ta Katsina United dai a karkashin shugaban kungiyar kwallon kafan wato Prince Abdussamad Badamasi ta sayo ‘yan wasa guda 12 gasu kamar haka:

Gambo Muhammed dan wasan gaba daga Kano Pillars.

Atule Joseph dan wasan gefe daga Kebbi United.

Manga Solomon dan wasan tsakiya daga Real Stars FC.

Giwa Isaac dan wasan baya bangaren hagu daga Elkanemi Warriors.

Ogene Elijah dan wasan baya daga Plateau United.

Habeeb Yakub dan wasan baya daga Rarara FC.

Abubakar Abdullahi Danja dan wasan tsakiya daga Rarara FC.

Aliko Mustapha mai tsaron gida daga Niger Tornadoes.

Alex Godwin dan wasan baya bangaren hagu dags Yobe Desert Stars.

Moses Ugwu dan wasan tsakiya daga Niger Tornadoes.

Nura Haruna dan wasan gaba daga ASN Niamey, Niger.

Muhammed Sani dan wasan gaba daga Kwara United

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan