Za a iya cewa abin yazo Inji mai kukan wanka domin kuwa a gobe Lahadi za a bude sabuwar kakar wasa.
Saidai kusan kowacce kungiyar kwallon kafa tayi gyara.
Akakar wasan data gabata dai kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ce ta zamo zakara inda ta lashe kofin karo na 8 a tarihi.

Ga jerin wasannin daza a fafata a ranar Lahadi:
Abia Warriors da Katsina United
Delta Force da Akwa Starlets
Enyimba FC da Nasarawa Utd amma an dage wasan.
FC Ifenyi Uba da Adamawa Utd
Heartland da Mountain Of Fire
Kano Pillars ta Rivers Unitedd
Plateau United daLobi Stars
Enugu Rangers da Sunshine Stars, shima wannan wasa an dage shi.
Warri Wolves da Akwa United
Wikki Tourist da Jigawa Golfing
Turawa Abokai
[…] Muƙalar Da Ta GabataSabuwar Kakar Wasan Ajin Premier ta Kasarnan […]