Yan Najeriya Miliyan 18 Ke Fama Da Cutar Daji – Hukumar Lafiya

148

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta ce kasar nan ce kasar da aka fi samun mace-macen masu fama da cutar cancer ko daji a nahiyar Afirka.


A cewar hukumar, rashin fadakarwa, da gano cutar a kurarren lokaci, da tsadar magungunan cutar, na daga cikin manyan dalilan da ke sa ake samun yawaitar mace-macen masu dauke da cutar ta daji a kasar na.


Wani Kwararren likita Aminu Aliyu ya ce “a tsakanin shekarar 2012, an samu karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar daga adadin miliyan 12 zuwa 14 har zuwa miliyan 18 a bara.”


Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, ba a fitar da alkaluman wannan shekara ba.

A irin matakan da take dauka, gwamnatn tarayya, ta kaddamar da wasu tsare-tsare na yaki da cutar, inda ko a farkon makon nan, ta ayyana zaftare kudaden da masu dauke da cutar za su kashe, wajen yin magani da kashi 50 cikin 100.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan