Buhari Ka Iya Neman Wa’adin Mulki Na Uku A 2023- Buba Galadima

212

Tsohon na hannun damar Shugaba Muhammadu Buhari a siyasance, kuma Shugaban Sabuwar Jam’iyyar APC, rAPC, Alhaji Buba Galadima, ya bayyana cewa kada ‘yan Najeriya su yi mamaki idan sun ga Shugaba Buhari ya sake yin takara a 2023.

Mista Galadima, wanda a halin yanzu ɗan ga-ni-kashe nin jam’iyyar PDP ne da kuma ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce makusantan Shugaba Buhari suna son tilasta masa ya yi takara neman wa’adin mulki na uku.

A wata tattaunawa da jaridar Sun, Mista Galadima ya yi iƙirarin cewa Shugaba Buhari ya cusa ɓangaren shari’a a aljihunsa, shi yasa ma ya tafi Saudiyya a jajibiren da Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci bisa ƙarar da Mista Atiku da PDP suka shigar.

A ta bakinsa: “Ban taɓa ganin irin wannan yanayi na tashin hankali ba kamar irin abinda muke gani a ƙarƙashin gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu. Ko a zamanin mulkin mallaka, da mulkin sojoji ‘yan Najeriya ba su sha wahala kamar haka ba.

“Da Buhari a kan mulki, kamar ‘yan Najeriya sun shiga motar bas ne mai dama ɗaya. Abin mamaki ma shi ne duk wahalar nan, da wahalar da ake ba ‘yan Najeriya, Buhari bai damu ba. Ba ya jin ma koke-koken wahalhalun da ake yi, waɗanda gwamnatinsa ta kawo wa ‘yan Najeriya.

“Yanzu ga shi Buhari ya ƙara yin tafiya ya bar ƙasar. Ya tafi Saudiyya, daga can kuma, zai wuce Birtaniya. Shin wannan ya dace da halayen shugaba na gari? Buhari yana ta yawo a ƙasashen duniya yayinda ‘yan Najeriya ke ci gaba da fama da raɗaɗin talauci.

“Wahalar da ake sha ba ta dame shi ba, ba ma haka ba, yana jin ƙwarin gwiwa cewa ya yi nasara a kotu. Ba don haka ba, da bai tafi Saudiyya ba a jajibiren da za a saurari ƙarar da Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ya shigar ba.

“Tuni Buhari ya cusa ɓangaren shari’a a aljihunsa, kuma yana tunanin ba abinda zai faru, kuma yana tunanin zai yi galaba a kotu. Gwamnatinsa ta lalata ɓangaren shari’a, kuma wannan abu ne mai haɗari ga dimokuraɗiyya, da ƙasarmu.

“‘Yan siyasa da yawa za su sha mamaki. Allah ne kaɗai Ya san me zai faru daga yanzu zuwa 2023. Wata ƙila wasu daga cikin hadiman Buhari za su tilasta masa ya shiga takarar 2023.

“Wata ƙila wasu daga cikin masu jin daɗi a ƙarƙashin gwamnatinsa su tilasta masa yin takara. An sha tilasta Buhari ya yi takara, kuma ba zan yi mamaki ba idan magoya bayansa suka tilasta masa zuwa takarar 2023.

“Amma, a fili yake, abinda waɗannan ‘yan siyasar dake neman takara da magana game da 2023 ba su sani ba shi ne, suna kunyata kansu ne. Suna fito da rauninsu a fili, kuma abokan takararsu ko magautansu na siyasa ka iya amfani da shi a kansu.

“Ba wanda ya san yadda 2023 za ta kasance. Allah ne kaɗai Ya sani. Komai zai iya faruwa daga yanzu zuwa 2023”.

A bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, ba wani mutum da za a iya zaɓar sa fiye da sau biyu a muƙani ɗaya a ɓangaren zartarwa.

Amma, an samu yunƙurin canza Kundin Tsarin Mulki a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo don ba ba shi damar ƙara yin takara, don ya yi shugabanci a karo na uku.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan