Kotun Ƙoli Ta Kori Ƙarar Walter Onnoghen

258

A ranar Litinin ne Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da aka ɗaukaka a gabanta, inda ake roƙonta ta yi bayani ko korar da aka yi wa tsohon Alƙalin Alƙalai na Ƙasa, CJN, Walter Onnoghen daga aiki tana bisa doka ko a’a.

Mai Shari’a Bode Rhodes-Vivour, wanda ya jagoranci alƙalai biyar, ya yi watsi da ƙarar da Dakta Samuel Nwawka ya shigar, bayan da mai ɗaukaka ƙarar ya kasa bayyana a gaban kotun, kuma babu wanda ya wakilce shi.

Mista Nwawka ya garzaya Kotun Ƙolin inda yake roƙon ta ta ƙarfafa Sashi na 22 na Dokar Kotun Ƙoli don warware matsaloli da yadda Gwamnatin Tarayya ta sallami Mista Onnoghen a matsayin CJN, ta hanyar wata ƙarar gaggawa da ta shigar a gaban Kotun Ɗa’ar Ma’aikata ranar 23 ga Fabrairu, 2019.

Mai ɗaukaka ƙarar ya roƙi Kotun Ƙolin da ta yi bayanin ko abinda waɗanda ake ƙara na ɗaya zuwa na shida suka wajen gabatar da buƙatar da kuma bada umarnin sallamar Mista Onnoghen kafin ya bayyana gaban Kotun Ɗa’ar Ma’aikata ko hakan ya yi dai-dai da tsarin mulki, ko suna da hurumi, ko ya keta doka.

Waɗanda ake ƙarar su ne Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, Mai Shari’a Tanko Mohammed, Dakta Mohammed Isah (Shugaban Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata CCB), Danladi Umar (Shugaban Kotun Ɗa’ar Ma’aikata CCT), Onorabul Julie Anabor (mamba a CCT), Hukumar Kula da Alƙalai ta Ƙasa, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da kuma Majalisar Dattijai a matsayin waɗanda ake ƙara na 1 zuwa na 9.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan