A ranar Litinin ne Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zama a Kaduna ta soke zaɓen ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Tudunwada da Doguwa ta jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa.
Mista Doguwa, wanda shi ne Shugaban Marasa Rinjaye, shi ne mutum na uku mafi muƙami a Majalisar Wakilai, banda Kakakin Majalisar da Mataimakin Kakakin Majalisar.
Kotun ta soke illahirin zaɓen a ƙananan hukumomi biyu da Mista Doguwa ke wakilta, saboda zaɓen cike yake da rashin bin ƙa’idoji.
A wani hukunci da gaba ɗaya gungun alƙalan kotun suka amince da shi, bisa jagorancin Mai Shari’a Oladotun Adefope-Okojie, kotun ta tabbatar da cewa ba a yi zaɓe ba, saboda jam’iyyun da ba a sa sunayensu ba.
Kotun ta ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta yi babban kuskure ta hanyar rubuta sakamakon jam’iyyu biyu kaɗai daga cikin jam’iyyu 53 da suka shiga zaɓen a Form EC8 (II) E.
[…] Muƙalar Da Ta GabataKotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Zaɓen Alhassan Ado Doguwa […]