Tafiye- Tafiyen Shugaba Muhammadu Buhari Riba Ko Faduwa? – Kawu Sule Rano

144

A ranar 2 ga watan Nuwamba ne na wannan shekara, sashen Hausa na BBC ya fitar da alkaluma na yawan kwanaki da kuma kasashe da Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarta tun bayan darewarsa mulki a shekarar 2015.

A kalla dai Shugaban ya ziyarci kasashe sama da talatin a tafiye-tafiyen da suka lakume sama da kwanaki dari hudu. Kusan idan aka kwatanta, za’a iya cewa daga cikin shekaru hadu da Shugaba Buhari yayi bisa karagar mulki fiye da shekara guda yayi ta ne a kasashen ketare yayin gudanar da irin wadancan ziyarce-ziyarce.

‘Yan Najeriya da dama dai sunyi korafi game da yawan zirga-zirga ta Shugaban a tsakankanin kasashen duniya, musamman ma duba da irin manyan kudade da ake kashewa wajen gudanar da su. Misali a kasafin kudi na wannan shekara Shugaban ya ware zunzuruntun kudi da yawan su yakai naira biliyan 3.3 domin tafiye-tafiyen sa dana mataimakin sa, a daidai lokacin da muhimman fannonin da suka rayuwar talakawa kamar na ilimi, kiwon lafiya dana noma ke fuskantar kwauro a wannan kasafi.

Haka na alkalumman hukumar dake sanya ido akan cigaban kasuwanci ta majalisar dinkin duniya sun nuna cewar daga shekarar 2015 zuwa 2018, Najeriya ta samu koma baya matuka a fannin zuba jarin kasashen waje, in da alkalumman hannayen jarin kasashen waje a kasar suka fadi daga dala biliyan 3.4 zuwa dala biliyan 1.9. Kenan ziyarce-ziyarce shugaban basu samar da cigaban da ake tsammani ba a fannin sanya hannun jari.

To amma wasu manazarta na ganin wadannan tafiye-tafiye da Shugaban ke yi a matsayin na dole, musamman duba da yadda kasar ta tsinci kanta cikin mashashsharar tattalin arziki a zangon farko na Shugaban.

Manyan misalai na riba da Najeriya ta samu sakamakon tafiye-tafiyen Shugaba Buhari zuwa kasashen ketare sune: (1) ziyararsa zuwa kasar Sin (China) inda ya kulla yarjajjeniyar da zata haifar da bada lamunin kudade ga Najeriya da yawan su yakai dalar Amurka biliyan 6; Sai kuma (2) ziyarar kwana-kwanan nan da yakai kasar Rasha (Russia) inda itama a cikinta ya kulla yarjajjeniyoyi da zasu bada damar bunkasa fannonin lantarki, noma, fetur da iskar gas, kauwanci, tsaro da ma’adanai.

Abin tambayar anan shine anya kuwa Najeriya zata iya cin moriyar wadannan abubuwan alkhairi da Shugaban ya farauto da ace yayi kwanciyarsa a Fadar sa ta Aso Rock? Shin da Shugaban yayi zamansa a fadar sa, da kuwa ya alkalumma game da zuba jari a Najeriya zasu kasance? Wannan na barwa mai karatu ya amsa.

Kawu Sule Rano, Malami Ne A Sashen Nazarin Halayyar Dan Adam Da Ke Jami’ar Bayero A Kano.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan