Home / Addini / UNICEF Ya Bada Tallafin Miliyan 105 Ga Makarantun Islamiyya Na Kano

UNICEF Ya Bada Tallafin Miliyan 105 Ga Makarantun Islamiyya Na Kano

Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya bada tallafin Miliyan N105 ga makarantun Islamiyya 440 a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, don haɓɓaka ilimin addinin Musulunci, a cewar jaridar Kano Focus.

Miki Koide, Ƙwararriyar Jami’ar Ilimi ta Ofishin UNICEF na Kano, ta bayyana haka ranar Lahadi yayin ƙaddamar da shirin tallafi ga makarantun Ƙur’ani da na Islamiyya a gidan gwamnatin jihar Kano.

Misis Koide ta ce UNICEF ya bada tallafin bunƙasa ilimi ga makarantun boko fiye da 300 da makarantun Ƙur’ani fiye da 420 da kuɗinsu ya kai Miliyan N180 da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Kano.

Haka kuma, Gwamna Abdullahi Umar Gabduje ya miƙa tallafin Miliyan N10 da kayan abinci ga alarammomi da aka zaɓo daga makarantun tsangaya 1000 a faɗin jihar Kano.

Gwamna Gabduje ya ce wannan tagomashi wani ɓangare ne na shirinsa na nada ilimin firamare da na sakandire kyauta kuma wajibi.

Ya ce tuni gwamnatin jihar Kano ta fara haɗe makarantun tsangaya da na boko wuri guda.

About Hassan Hamza

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *