Wani Mutum Ya Yi Yunkurin Kashe Jikarsa Sabo Da Tsoron Talauci

184

Hukumar ‘yan sanda a birnin Haydarabad dake kasar Indiya ta kama wani tsoho da abokinsa yayinda suke yunkurin rufe jikanyarsa da ranta.

A yayinda kakan yarinyar da abokinshi ke gina kabari a cikin ciyawar da zasu rufe jaririyar ne wani mutun cikin motarsa ya hangesu. Ya kuma lura da a hannun dayansu akwai bargo da jaririya mai rai lullube a ciki. Nan take ya sanar da ‘yan sanda mafi kusa. ‘Yan sandan sun tarar da kakan mara tausayi da abokinsa a lokacin da suke kokarin aikata wanan ta’asar.

A lokacin da aka lura da cewa jaririyar mai rai ce an kai ta asibiti mafi kusa domin kula da lafiyarta.

An bayyana cewa a ‘yan shekarun nan ana yawan samun bakadalar rufe jarirai mata da ransu a kasar Indiya.

Ana dai yawan bayyana mata a matsayar lalura kasancewar al’adan kasar mata ke biyan sadaki a lokacin aurar dasu.

A ‘yan kwanakin da suka gabata an tono wata jaririyar da aka rufe da ranta a wani yankin jahar Uttar Pradesh dake kasar ta Indiya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan