Za A Ci Gaba Da Rufe Boda Har Sai Gwamnati Ta Cimma Manufarta- NCS

111

Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS, ta ce rufa bakin iyakar da ta yi na ɗan lokaci zai ci gaba har sai an cimma manufofin da suka sa aka rufe.

Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Hukumar, Joseph Attah ya bayyana haka yayinda yake mayar da martani ga wata gajeruwar sanarwa da hukumar ta ba kafafen watsa labarai.

A wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Abuja ranar Lahadi, Mista Attah ya bayyana cewa gajeruwar sanarwar ta cikin gidan tana nufin kawo ƙarshen wani rukuni na aikin haɗin gwiwa na tsaro da aka sa wa suna: “Ex Swift Response”.

A ta bakinsa, sanarwar ba tana nufin kawo ƙarshen rufe bakin iyakar ba.

Ya ce yawanci irin wannan aiki na tsaro ana yin sa ne rukuni-rukuni.

NAN ya bada rahoton cewa a kwanan nan ne Kwanturola Janar na NCS, Kanar Hameed Ali ya ce babban maƙasudin da yasa aka rufe bodar shi ne a tabbatar da cewa ƙasashe maƙotan Najeriya sun bi yarjejeniyar zirga-zirga ta Hukumar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS.

Mista Ali ya bayyana cewa yarjejeniyar zirga-zirga ta tilasta hukumomin kula da shige da fice a maƙotan ƙasashe su riƙa rako kaya da za a kawo Najeriya bodar Najeriya don kar waɗanda suka shigo da su su ƙi biyan kuɗin kaya.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa rufe bodar ya taimaka wajen rage yawan hare-hare da mahara ke kaiwa.

Ya ce matakin rufe bodar ya kuma taimaka wajen hana shigo da makamai da albarusai zuwa ƙasar nan.

Sanarwar ta ta ɓulla daga Kwanturola mai kula da bin doka na Hukumar Kula da Shige da Ficen ta Ƙasa, NCS, Victor Dimka, mai ɗauke da kwanan watan 1 ga Nuwamba, dake yawo a kafafen watsa labarai ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙara lokacin rufe boda zuwa watan Janairu na 2020.

Mista Dimka ya bayyana a gajeruwar sanarwar ta cikin gida cewa rufe bakin iyajokin na ƙasa ya samu “gagarumar nasara”.

Ya ce amma har yanzu kawai wasu manufofi da ba a cimma, dalilin da yasa aka ƙara lokacin.

“An umarci da in sanar da kai cewa duk da gagarumar nasarar da aikin rufe bodar ya samu, musamman alfanu ta ɓangaren tattalin arziƙi da tsaro ga ƙasar nan, har yanzu ba a cimma wasu manya-manyan manufofi ba.

“A bisa wannan ne, Shugaban Ƙasa ya amince da a ƙara wa’adin rufe bodar zuwa 31 ga Janairu, 2020.

“Sakamakon haka, ana buƙatar ka da ka isar da wannan ci gaba ga dukkan ma’aikata don su sani kuma su sa mu jagoranci.

“Haka kuma, nan ba da daɗewa ba za a biya alawus-alawus na kula da ma’aikata da zuba mai a motoci a tsawon lokacin wannan ƙari.

“Wannan don ka sani ne, ka ɗau matakin da ya dace”, in ji gajeruwar sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan