Ganduje Ya Raba Wa Sabbin Kwamishinoninsa Muƙamai

199

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sake naɗa mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin Kwamishinan Aikin Noma, kamar yadda ya ƙara naɗa Murtala Sule-Garo a matsayin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi.

Haka kuma, tsohon Kwamishinan Shari’a, Ibrahim Mukhtar zai ci gaba da riƙe muƙaminsa.

Dama a yau ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da sunayen kwamishinoni 20 da gwamna ya tura mata.

Daga bisani ne gwamnan ya rantsar da kwamishinonin a Rufaffen Ɗakin Wasa na Filin Wasa na Sani Abacha.

Majiyoyi a gidan gwamnati sun ce a daren nan ne gwamnan zai yi taron Majalisar Zartarwa na farko da sabbin kwamishinonin a Fadar Gwamnatin Kano.

Ga sunayen sabbin kwamishinonin da muƙamansu:

 1. Dakta Nasiru Yusuf Gawuna
  Kwamishinan Aikin Noma
 2. Onorabul Murtala Sule Garo Kwamishinan Ƙananan Hukumomi
 3. Injiniya Muazu Magaji
  Kwamishinan Ayyuka
 4. Barista Ibrahim Muktar
  Kwamishinan Shari’a
 5. Onorabul Musa Iliyasu Kwankwaso
  Kwamishinan Raya Karkara
 6. Dakta Kabiru Ibrahim Getso
  Kwamishinan Muhalli
 7. Kwamared Mohammed Garba
  Kwamishinan Yaɗa Labarai
 8. Onorabul Nura Mohammed Ɗankadai
  Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare
 9. Onorabul Shehu Na’Allah Kura
  Kwamishinan Kuɗi fa Bunƙasa Tattalin Arziƙi
 10. Dakta Mohammed Tahar Adam
  Kwamishinan Harkokin Addini
 11. Dakta Zahara’u Umar
  Kwamishiniyar Harkokin Mata
 12. Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa
  Kwamishinan Lafiya
 13. Onorabul Sadiq Aminu Wali
  Kwamishinan Albarkatun Ruwa
 14. Hon Mohammed Bappa Takai
  Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha
 15. Onorabul Kabiru Ado Lakwaya
  Kwamishinan Matasa Da Wasanni
 16. Dakta Mariya Mahmoud Bunkure
  Kwamishiniyar Ilimi Mai Zurfi
 17. Onorabul Ibrahim Ahmed Ƙaraye
  Kwamishinan Yawon Buɗe Ido da Al’adu
 18. Onorabul Muktar Ishaq Yakasai
  Kwamishinan Ayyuka na Musamman
 19. Onorabul Mahmoud Muhammad
  Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu
 20. Onorabul Muhammad Sunusi Saidu
  Kwamishinan Ilimi
 21. Barista Lawan Abdullahi Musa
  Kwamishinan Gidaje da Sufuri
Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan