Kano 9: Ƙungiyoyin Mata Sun Miƙa Koke Ga Majalisar Dokokin Jihar Kano

266

Tawagar wakilan ƙungiyoyin mata 20 ne suka taru a Majalisar Dokokin Jihar Kano ranar Talata, inda suke neman majalisar ta tsoma baki bisa garkuwa da kuma gano yara ‘yan asalin Kano tara da aka yi kwanan nan.

Ƙungiyoyin, bisa Gamayyar Malamai da Ƙungiyoyin Da Ba Na Gwamnati Ba, NGOs, sun yi kira ga malalisar da ta kafa kwamitinta mai zaman kansa don bincikar lamarin.

Jagorar wakilan, Amira Shitu-Abdulwahab, ta ce manufar kiran shi ne a gano duk wani naƙasu a cikin dokokin da ake amfani da su a halin yanzu waɗanda ke ba masu aikata laifi damar aikata irin waɗannan munanan laifuka.

Ta bada shawarar cewa “idan an gano naƙasu,, sai majalisar ta gaggauta wajen yin kwaskwarima ko zuwa da sabbin dokoki don magance matsalar gaba ɗaya, hukuncin kisa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada shawara ya yi dai-dai a wannan batu”.

Ƙungiyoyin sun kuma yi kira ga malalisar da ta bibiyi Kwamitin Bincike na Jihar Kano da aka kafa game da batun, ta kuma tabbatar gwamnatin jiha ta yi abinda ya dace game da irin shawarwarin da za su fito daga rahoton kwamitin.

Jagorar ta kuma ce a matsayin wani ɓangare na taron tattaunawa da suka yi kwanan nan, sun bada shawarar cewa ya kamata Majalisar ta gaggauta ganin cewa rayuwar yaran ta inganta, ta kuma tabbatar gwamnati ta aiwatar da dukkan manufofi da gwamna ya tsara game da yaran.

“Muna kuma yin kira ga Majalisar da ta zartar da wata doka da za ta yi kira ga gwamnatin jiha ta ba dukkan hukumomin tsaro a jihar nan goyon baya a wani yanayi da zai sauƙaƙa gano sauran yaran da aka sace.

“Ya kuma kamata Majalisar ta yi duba zuwa yiwuwar kulle dukkan gidajen dake ajiye masu garkuwa da mutane, sannan a tuhumi waɗanda suke ba su haya.

“Haka kuma, ya kamata Majalisar ta umarci gwamnatin jiha ta janye wakilcin sauran al’ummomin Ibo da na Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, saboda ba mu ga hikimar sa su a wani al’amari da ya shafi Kano kaɗai ba”, in ji ta.

Da yake mayar da jawabi, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Abdul’azeez Garba Gafasa, ya yaba wa ƙungiyoyin bisa irin dattakon da suka yi wajen tafiyar da wannan al’amari.

A ta bakinsa, garkuwa da yara daga jihar Kano zuwa wasu jihohin Kudu da kuma canza musu addini abu ne mai ban takaici da yake buƙatar kulawar gaggawa daga dukkan ɓangarori.

Mista Gafasa ya ƙara da cewa majalisar za ta warware matsalar da nufin kawo ƙarshen irin wannan munanan laifuka a jihar.

Kakakin ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin da su ako da ƙudurori da za su bunƙasa rayuwar mata da yara a jihar, yana mai ba su tabbacin mayar da su doka cikin gaggawa.

Ya kuma tabbatar wa ƙungiyoyin cewa majalisar za ta bibiyi aikin kwamitin da gwamna ya kafa saboda ‘yan majalisar ma suna cikin kwamitin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan