Majalisar Dokokin Kano Ta Tantance Dukkan Kwamishinonin Ganduje

231

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da sunayen kwamishinoni 20 da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tura mata sunayensu.

Majalisar ta tantance kwamishinonin ne bisa jagorancin Kakakinta, Abdulazeez Garba-Gafasa.

An kuma shafe kimanin sa’o’i uku ana tantancewar.

Wasu daga cikin waɗanda aka miƙa sunayen nasu, waɗanda a lokutan baya ‘yan majalisa ne, an ba su ‘yan mintuna kaɗan ne don su yi bayanin nasarorinsu.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Litinin ne Kakakin Majalisar ya sanar da karɓar sunayen kwamishinonin daga gwamna, takwas daga cikinsu tsaffin kwamishinoninsa ne.

Daga cikin waɗanda suka yi aiki a gwamnatin da ta gabata da akwai tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Muhammad Garba da na Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule-Garo.

Sauran su ne Ibrahim Mukhtar, Musa Iliyasu-Kwankwaso, Kabiru Ibrahim-Getso, Shehu Na’Allah-Kura, Mukhtar Ishak-Yakasai da Muhammed Tahir-Adam.

Sabbi su ne Ma’azu Magaji, Nura Muhammad-Dankade, Zahra’u Umar-Muhammad, Aminu Ibrahim-Tsanyawa, Sadiq Aminu-Wali, Muhammad Baffa-Takai da Kabiru Ado-Lakwaya.

Sauran su ne Mariya Mahmoud-Bunkure, Ibrahim Ahmad-Karaye, Mahmoud Muhammad-Dansantsi, Muhammad Sanusi-Sa’id da Lawan Abdullahi-Musa.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan