A ranar 5 ga Nuwamba 1955 aka haife shi a unguwr Kurmawa ta birnin Kano

Yana da shekara 22 ya gama digirin farko
Yana da shekara 23 aka dauke shi aiki
Yana da shekara 25 ya zama firinsifal
Yana da shekara 26 Rimi ya sanya shi cikin kwamitin masanan gidan Santsi
Yana da shekara 33 ya zama shugaban kungiyar firinsifals ta Najeriya
Yana da shekara 34 ya zama darakta
Yana shekara 39 ya zama babban sakatare
Yana shekara 46 ya yi ritaya daga aiki
Yana shekara 46 ya zama gwamnan Kano
A shekara 50 ya maimaita mulkin Kano
A shekara 54 ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ANPP
Yana shekara 55 ya jagoranci ANPP wajen kafa jam’iyyar APC
A shekara 59 ya zama ministan ilimi
A shekara 63 ya zama sanata a majalisar dattijai
A ranar Talata mai zuwa
5 ga watan Nuwamba 2019
Sardaunan Kano, Sanata Mallam Ibrahim Shekarau zai cika shekara 64 a duniya
