Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta shirya tsaf don fara kashe miliyan N350 duk wata game da Shirinta na Ciyar da Ɗalibai da zai haɗa da ɗaliban aji 4 zuwa 6.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Gabduje ya bayyana haka ranar Litinin a yayin ƙaddamar da shirin a makarantar Child Friendly Initiative School dake Wudil.
“Yayinda Gwamnatin Tarayya ke ciyar da ɗaliban firamare daga aji 1 zuwa 3, wannan gwamnati za ta faɗaɗa shirin don ya haɗa da ɗaliban aji 4 zuwa 6, wanda zai laƙume miliyan N350 duk wata”, ya bayyana haka.
Wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, gwamnan ya bayyana cewa a ƙaramar hukumar Wudil kaɗai, ana sa ran ɗalibai 16,192 daga makarantun firamare 56 za su amfana da shirin ciyarwa.
Ya ce gwamnatinsa ta kafa Kwamitin Ciyar da Al’umma Gaba, CPC, a masarautu biyar da kuma yankunan ƙananan hukumomi 44 na jihar don tabbatar da cewa shirin gwamnatin jihar na ilimin firamare kyauta kuma wajibi ya cimma gaci.
A kan shirin tsangaya, Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa dukkan malaman da aka ɗauka waɗanda aka tantance sun fara karɓar alawus-alawus, kuma an samar musu da dukkan kayan aikin da suke buƙata don inganta ayyukansu.
“Mun ɗauki malaman Islamiyyu waɗanda suka cancanta kawo yanzu, waɗanda za su koyar da ɗaliban ilimin tushe game da Musulunci”, in ji shi.
Gwamnan ya shawarci masu hannu da shuni daga ƙararmar hukumar ta Wudil da su haɗa kawunansu wuri ɗaya, su haɗa kai da gwamnati don tabbatar da nasarar shirin.
Tunda farko, shugaban ƙaramar hukumar Wudil, Sale Kakkausa ya gode wa gwamnan jihar bisa ɗaga darajar ilimi a jihar.
Shi ma, Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulkadir ya yaba da da ƙoƙarin gwamnatin jihar bisa kyawawan manufofinta.
[…] Muƙalar Da Ta GabataShirin Ciyar Da Ɗaliban Firamare Zai Riƙa Laƙume Miliyan 350 Duk Wata- Ganduje […]