Buhari Ya Sallami Hadimai 35 Daga Aiki A Ofishin Osinbajo

327

Kwana ɗaya bayan ya rattaba ga wata doka da za ta inganta harkar haƙar mai a teku mai suna Deep Offshore and Inland Basin Production Sharing Contract Amendment Bill, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sallamar a ƙalla hadimai 35 daga aiki, daga cikin sama da hadimai 80 a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, a cewar majiyarmu.

A halin yanzu dai, Shugaban yana Landan, Ingila, inda yake wata ziyarar “ƙashin kai” ta tsawon makonni biyu, kuma ana sa ran dawowarsa zuwa Abuja ranar 17 ga Nuwamba.

Majiyarmu ta ce hadiman da sallamar ta shafa, waɗanda aka ba su takardun ɗaukar aiki a Agusta, sun haɗa da wasu Manyan Mataiamka na Musamman, Mataimaka na Musamman da sauransu.

Sahihan majiyoyi waɗanda suka nemi a ɓoye sunayensu sun ce za a iya ba hadiman takardun sallama daga aiki a yau Laraba.

Tun kafin korar tasu, majiyarmu ta ce an tura hadiman zuwa wasu ma’aikatu da suka yi dai-dai da muƙamansu a watan da ya gabata. Ana zargin an yi haka ne don a hana su shiga Villa, Fadar Shugaban Ƙasa, a kuma rage tasirin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

“Koda yake dai fiye da rabin hadiman suna karɓar albashi ne daga hukumomi masu bada tallafi, “shafaffu da mai” sun kore su don rage tasirin Mataimakin Shugaban Ƙasa”, a cewar wata majiya dake da masaniyar yadda al’amura ke gudana.

“Ba wanda aka tuhuma ko samu da wani kuskure. Ba magana ce ta rage kashe kuɗaɗe ba, saboda ba wani da aka kora daga Ofishin Shugaban Ƙasa ko kuma Ofishin Uwar Gidan Shugaban Ƙasa, inda aka naɗa ƙarin hadimai shida a cikin ƙasa da wata ɗaya da ya gabata. Kawai an sallame su ne don a rage tasirin Mataimakin Shugaban Ƙasa”, in ji majiyar.

Masu magana da yawun Shugaban Ƙasa da Mataiamkin Shugaban Ƙasa, Garba Shehu da Laolu Akande ba su bada amsa ba ga saƙon waya da aka aika musu don jin ta bakinsu game da wannan turka-turka.

Wahalhalun Da Osinbajo Ke Fuskanta

Kamar dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban Ƙasa da Mataiamkinsa tun lokacin da aka fara wa’adin mulki na biyu, inda Shugaban Ƙasar ya mayar da wasu hukumomin dake ƙarƙashin Mista Osinbajo zuwa ofishinsa ko wasu ma’aikatu.

Masana yadda al’amura ke gudana a Fadar Shugaban Ƙasa sun ce wasu masu faɗa a ji, da aka fi sani da “shafaffu da mai” sun fusata da wasu manya-manyan matakai da Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ɗauka a lokacin da Shugaban Ƙasa ba ya nan.

An yi amannar cewa mafi girma daga “laifukan” Mista Osinbajo shi ne sallmar Lawal Daura, tsohon Darakta Janar na Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, SSS, lokacin da Mista Osinbajo ke Muƙaddashin Shugaban Ƙasa a watan Agustan bara.

Wani mataki da ya jawo fushin “masu faɗa a jin” shi ne aika wasiƙa zuwa ga Majalisar Dattijai da Mista Osinbajo ya yi a watan Fabrairu, 2017, inda ya buƙaci a tabbatar da naɗin Alƙalin Alƙalai na Ƙasa, CJN a wancan lokaci, Walter Samuel Onnoghen.

Amma Shugaban Ƙasar ya fara nuna ƙarfin mulki ne lokacin da ya janye Shirye-Shirye Walwalar Jama’a, SIPs daga Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa zuwa sabuwar Ma’aikatar Jin Ƙai, Kare Afkuwar Annoba da Walwalar Jama’a.

Shirye-Shiryen na Walwalar Jama’a sun haɗa da TraderMoni, Shirin Ciyar Da Ɗalibai, N-Power da sauransu.

A ranar 16 ga Satumba, Shugaba Buhari ya maye gurbin Majalisar Gudanar da Tattalin Arziƙi da Mista Osinbajo ke jagoranta da Majalisar Bada Shawara Kan Tattalin Arziƙi wadda kai tsaye za ta riƙa kai rahoto Ofishin Shugaban Ƙasa.

A cewar wani rahoto da jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa ranar Talata, hatta shirin kafe Ruga mai cike da cece-ku-ce, an ƙwace shi daga hannun Mista Osinbajo bayan shawarar da Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ƙasa, Abba Kyari ya bayar.

Koyi Da Obasanjo?

Jim kaɗan bayan an rantsar da tsohon Shugaban Ƙasa, Olesegun Obasanjo a wa’adin mulki na biyu a watan Mayu, 2003, sai dangantakarsa da Mataiamkinsa, Atiku Abubakar ta fara tsami bisa zargin Atiku da ƙoƙarin yin takara da shi a zaɓen fitar da gwani na PDP.

A lokacin da al’amura suka yi zafi, sai Mista Obasanjo ya sallami hadiman Mista Atiku don ya daidaita al’amuransa na siyasa.

Waɗanda Mista Obasanjo ya sallama a watan Yuli na 2006 sun haɗa da Adeolu Akande, Onukaba Adinoyi-Ojo, Chris Mammah, Shina Ayati, Sam Oyovbaire, Lawal Jafaru Isa da Garba Shehu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan