Gwamna Ganduje Ya Bukaci Sababbin Kwamishinoni Da Su Kasance Masu Gaskiya Da Rikon Amana

199

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci sabbin kwamishinonin da aka rantsar da su gudanar da ma’aikatunsu cikin wayewa, tare da kudirin kai jihar zuwa ga matakin cigaba.

Da yake magana a taron rantsar da sabbin kwamishinonin guda 20, Ganduje ya bukace su da su kasance masu sa idanu, fasaha, gaskiya da kuma jajircewa wajen gudanar da ma’aikatunsu mabanbanta.

Ganduje ya ce: “Mutanen Kano suna fatan samun cigaba daga gare ku, muna sanya ran za ku kasance masu gaskiya, fasaha da jajircewa akan hakkokin da suka rataya a wuyanku. Kuma muna sa ran za ku yi iya bakin kokarinku domin kai jihar Kano zuwa mataki na gaba.

“Ku kasance tsararru sosai, masu fasaha domin ku bayar da gudunmawarku wajen cigaban tattalin arzikin Kano. Ana sanya ran za ku yi aiki a matsayin tawaga tare da sakatarorin dindindin da daraktoci domin aiwatar da manufofinmu da kyau. Ana sanya ran za ku mutunta kujerunku da kuma aiki kai da fata tare da jama’a.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan