Nan Gaba Kaɗan Najeriya Za Ta Fara Fitar Da Shinkafa- Dangote

344

Kamfanin Dangote ya yi alƙawarin canza Najeriya daga ƙasar dake shigo da shinkafa zuwa ƙasar da za ta riƙa fitar da shinkafa.

Kamfanin ya ce gonakinsa na shinkafa masu faɗin hekta 150,000 a jihohin Jigawa, Kano, Kebbi, Nasarawa, Naija, Sakkwato da Zamfara da kuma kamfanonin shinkafa 10 da yake kafawa a sassa daban-daban na ƙasar nan za su riƙa samar da tan miliyan ɗaya na shinkafa duk shekara.

Babban Daraktan Kamfanin Dangote, Kunt Ulvmoen, ya bayyana haka, lokacin da ya yi wa kaftin-kaftin na kasuwanci da masana’antu jawabi a ranar Kamfanin Dangote ta Musamman a ci gaba da Bikin Kasuwar Duniya ta Legas Karo na 33.

A ta bakin Mista Ulvmoen, an san kamfanin da zama lamaba ɗaya a kasuwancin shinkafa a Najeriya har lokacin da ya ɗauki matakin dakatar da kasuwancin duk wani kaya wanda ba zai ƙara wa kayan gida daraja ba.

“Duk da haka, har yanzu abokan ciniki suna tambaya ina shinkafar Dangote shekaru bayan kamfanin ya ɗauki matakin daina shigo da shinkafa”, in ji shi.

“To yaya za mu yi? Za mu shiga noman shinkafa da kuma sarrafawa, kuma za mu ci gurin samar da tan miliyan ɗaya duk shekara.

“Tuni mun fara aiki a gonaki. Tuni mun samu wata shinkafa samfarera a cikin rumbuna. Kuma muna ƙalubalantar sauran da su yi abinda muka tsara za mu yi don mayar da shinkafa abinda kowa zai iya siya a Najeriya”, in ji Mista Ulvmoen.

“Abinda yake da muhimmanci sosai a Najeriya shi ne gas. Har yanzu akwai gas da yawa a wajen haƙar man fetur da har yanzu ba a ƙona shi ba. Amma wannan gas ɗin yana da muhimmanci sosai wajen samar da makamashi a ƙasar nan. Kuma muna so mu tabbatar cewa akwai gas a cikin fayif. Najeriya na buƙatar alkinta dukkan albarkatun ƙasa musamman fetur da gas.

“Muna da kamfanin sikari a Apapa da zai iya samar da tan miliyan 1.4 duk shekara. Amma, kuma muna son rage shigo da ɗanyen sikari. Saboda haka muna haɓɓaka nomanmu na rake. Muna so Najeriya ta zama mai dogaro da kai daga shigo da sikari.

“Muna samar da ayyuka. Idan kana so ka rage garkuwa da mutane ko ta’addanci, dole ka sama da ayyuka. Ba wanda ke so yin haka idan zai iya kauce masa”, ya ƙara da haka”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan