Shan Abarba Na Rage Hadarin Kamuwa Da Cutar Kansa

312

Cibiyar bincike akan ilimin shuke-shuke wato National Horticultural Research Institute (NIHORT) ta ce yawan shan Abarba na rage yiwuwar kamuwa da cutar daji kuma yana sa saurin warkewa daga jinyar tiyatar cutar.

Shugaban shugaban cibiyar ta NIHORT Dakta, Abayomi Olaniyan ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da cibiyar raya Abarba a Owo, karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Diraktan, wanda ya smau wakilcin Dakta Olutola Oyedele daraktan binciken NIHORT, ya ce Abarba na daya daga kayan marmari mai muhimmanci ga lafiyar jiki da kuma tattalin arzikin kasa.

Yace: “Abarba na kunshe da sinadarai da dama na inganta garkuwa jiki. Yawan shan Abarba na sa saurin warkewa daga jinyar tiyata kuma yana taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da cutar kansa.”

A karshe ya bukaci al’ummar da su rungumi no man abarba domin inganta tattalin arzikin kasar nan, tare da samar da ita a fadin kasuwannin kasar nan.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan