Dandazon Mata Sun Gudanar Da Zanga-zangar Lumana Tsirara A Jihar Ondo

225

Dandazon yan kasuwa mata a garin Igbokoda, hedkwatar karamar hukumar Illaje da ke jihar Ondo sun yi zanga-zanga akan yunkurin gwamnatin jihar na rushe wasu gine-gine da aka yi a babbar kasuwar Igbokoda.

Zanga-zangar wacce ta dauki tsawon sa’o’i hudu, ta jawo cushewar manyan titunan garin sakamakon shinge da masu zanga-zangar su ka saka a titunan shiga kasuwar garin.

Tun da farko jami’an gwamnatin jihar ta Ondo sun yi yunkurin rushe gine-ginen da aka yi su ba bisa ka’ida ba. Wanda hakan ya sanya matan yin zanga-zangar.

Babban sakataren cibiyar kasuwancin gwamnatin jihar Ondo, Mista Sunday Lebi, ya ce gwamnatin ba za ta lamunci rashin biyayya ba. Ya ce, gwamnati ta fusata da abinda matan suka yi da ya hana jami’an aiwatar da abinda ya kaisu kasuwar.

Ya kara da cewa, jami’an gwamnatin sun kasa aiwatar da nufinsu saboda tsirara da matan suka yi yayin zanga-zangar kuma sun yi amfani da miyagun kalamai akan jami’an.

Yace, cibiyar na da damar maida kasuwar yadda ya dace domin samun damar karuwar kudin shiga ga lalitar gwamnatin jihar.

“mun je domin yin abinda ya kamata bayan mun tattauna dasu tare da sanar da su an yi hakan ga sauran kasuwannin jihar. Gini ba bisa tsari da ka’ida ba yana lalata kasuwa kuma hatsari ne ga rayuka da ababen hawa dake shige da fice a kasuwar.”

A karshe babban sakataren yace, gwamnatin jihar za ta cigaba da amfani da hanyoyin da ya dace domin tabbatar da kasuwannin gwamnatin jihar sun kasance cikin halin da ya kamata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan