Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje, ta samu nasarar samun matsayi na ɗaya a cikin wata gasa da kamfanin mai na kasa NNPC ya shirya a tsakanin maza da mata, dattijai da matasan.


Taron wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja karkashin shugaban rukunin kamfanin na (NNPC) Mallam Mele Kolo Kyari, wanda ya samu wakilcin babban jami’in gudanarwa na hukumar, Mallam Farouk Sa’id.
Farouk Sa’id ya miƙawa Balaraba Abdullahi Ganduje lambar yabon a madadin kamfanin gaba ɗaya saboda wannan gagarumar nasara da ta samu.
Taron ya samu halartar manyan ma’aikatan Kamfanin na NNPC da sauran jami’an gwamnati da yan kasuwa.
Turawa Abokai